Yi wa fursunoni afuwa: Ganduje adalin shugaba -Kanawa da fursunoni

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Sakamakon kokarin da gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ke yi wajen yi wa masu laifuffuka afuwa, al’ummar jihar Kano da wakansu daga cikin fursunonin da gwamnan ya yi wa afuwa, sun bayyana gwamna Ganduje a matsayin shugaba adali mai kishin al’umarsa.

A cikin wata tattaunawa da wakilinmu ya gudanar, al’ummar Kano da kuma fursunoni sun bayyana cewa, wajibi ne a yaba wa gwamna Ganduje, saboda adalcinsa da kuma kokarin ganin kowa yana zaune cikin yanayi mai kyau, musamman a wannan karni da ake ciki.

Sannan mafiya yawan mutanen da Albishir ta tattauna da su, sun sanar da cewa, a duk fadin kasa, babu gwamnan da ya yi wa fursunoni afuwa kamar gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje, saboda tausayin da yake da shi da kuma kishin al’umarsa.

Da muka zanta da Malam Dauda Mohammed Ali, ya nunar da cewa, tun hawansa kujerar gwamnan jihar Kano, gwamna Ganduje yake yi wa fursunoni afuwa tare da tallafa masu domin su ci gaba da rayuwa mai albarka kamar kowane dan kasa kuma cikin ’yanci.

Sannan ya jaddada cewa, yadda gwamna Ganduje yake yi wa fursunoni afuwa ko shakka babu za a sami kwanciyar hankali da karuwar arziki a wannan kasa, idan har gwamnoni suka dauki tsari irin na gwamnan jihar Kano lallai za a sami ci gaba da kuma rage cunkoso a gidajen yari.

Daga bisani Malam Dauda Mohammed ya kuma ya wa gwamnan godiya da fatan alheri. Shi ma a nasa tsokacin, wani fursuna da aka yi wa afuwa, Malam Sani Lawal, ya bayyana cewa, babu shakka shirin yin afuwa na mai girma gwamna, Dokta Abdullahi Umar Ganduje shi ne ake bukata daga shugabanni, kuma hakan yana taimakawa wajen canza rayuwar al’umma kamar yadda ake gani cikin shekaru 7 da gwamna Ganduje ya yi yana mulkin jihar Kano.

Wakilinmu wanda ya gudanar da bincike dangane da afuwar da ake yi wa fursunoni a jihar Kano, ya ruwaito cewa, kusan dukkanin fursunonin da gwamnan Kano ya yi wa afuwa suna ci gaba da rayuwarsu bisa sanin yakamata, sannan ya zuwa yanzu, gwamna Ganduje ya yi wa fursunoni 3,898 afuwa wanda hakan abin a yaba masa ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *