Yobe ta ja damarar shimfida ayyukan raya kasa -Umar Goneri

Tura wannan Sakon

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnatin Jihar Yobe karkashin gwamna Mai Mala Buni ta dukufa matuka wajen shimfida ayyukan raya yankunan jihar da hasken lantarki musamman yankunan karkara da aka bar su a baya.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin babban manajan hukumar kula da samar da hasken lantarki a yankunan birane da karkara REB na jihar, Injiniya Umara Mustapha Goneri, a tattaunawarsa da wakilinmu a garin Damaturu.

Injiniya Umara Goneri ya kara da cewa, ayyukan da suke gudanarwa ba su tsaya ga yankunan karkara kadai ba, sukan gudanar da ayyukansu a cikin biranen jihar matukar bukatar hakan ta taso musamman kan abin da ya shafi birane a karkashin tsarin da ake kira “Serbe and under serbed” ma’ana shi ne, akwai wasu ayyukan sanya lantarki a wasu manyan garuruwa, amma saboda bunkasuwar garuruwa da yawan gine-gine ya jawo karin bukatar isar musu da lantarki. Sannan da wuraren da an riga an ja musu lantarkin amma ta yi musu kadan matuka saboda yawan al’umommin da ke wuraren.

Har ila yau, akwai garuruwa da ba a taba kai musu lantarki ba, musamman yankunan karkara. Haka kuma, akwai asibitocin da muke da su a cikin wannan jihar, wadanda suna bukatar karin hasken lantarki dare da rana, wanda zai taimaka wajen gudanar da aikaceaikacen kula da majinyata, bayan hasken lantarkin a asibitocin, ga samar da ruwa, a samu damar ajiye magunguna na musamman tare da gwaje-gwaje da aune-aune da sauran ayyukan da ba za su yiwu ba sai da lantarki a asibitocin jihar.

Kuma sanin kowa ne cewa, zuwan gwamnatin gwamna Mai Mala Buni a jagorancin jihar, ya taka muhimmiyar rawa wajen bai wa hukumar tamu cikakken goyon baya, musamman saboda yadda ayyukanmu suka shafi rayuwar talakawa kuma da kansa ya kira mu tare da ba mu umurnin cewa, mu shiga kowane lungu na jihar domin mu kai ci gaba a kauyukan da ya dace a ce sun more romon dimukuradiyyar da ake gudanar da ita a jihar.

Wannan goyon bayan da muka samu daga gwamna Buni hakan ya sa mun tashi wurjanja domin aiwatar da umurnin gwamnan, wanda a wannan dan karamin zaman tattaunawar da muke yi ba zai yuwu na iya lissafa maka adadin ayyukan da muka aiwatar ba, saboda zai kai mu tsawon lokaci muna yi.

Amma duk da haka, a takaice, mun gudanar da aikace-aikacen sanyawa da fadada hasken lantarki a wasu manyan garuruwan jihar Yobe, wadanda suka hada da Damaturu da Gashu’a da Nguru da Buni Yadi da Potiskum da kuma Geidam. Haka nan inda suke da lantarki, wanda daga baya sun fuskanci matsaloli daban-daban na na’urorin rarraba hasken lantarki (Transformer) ko turakun jawo wutar lantarkin, wanda ko a wannan makon kadai, taransifoma kimanin hudu muka raba a unguwannin Mazagane da unguwar Jangam a Gadaka da unguwar Tandari Potiskum da kuma unguwar Jaji, duka a Potiskum, wadanda a cikin mako guda muka gudanar da wannan aikin.

Ina ga ayyukanmu na shekara uku da rabi, wanda idan muka ce zamu lissafo su aiki ne ba karami ba matuka. Har ila yau, a kauyukan da muka ja wa layukan lantarki, wadanda ba a taba kai musu wutar ba a nan jihar Yobe, sun kai sama da 30, kadan daga cikinsu sun hada da; kauyen Sumsuma, kauyen Kasaisa, kauyen Mallam Adamu, kauyen Mirwa, da kuma kauyen Zubak da su Lawan Kalam, da makamantansu.

Suna nan da yawan gaske, wanda hukumar raya yankunan karkara da wutar lantarki a jihar Yobe, ta gudanar da ayyuka sama da 100 cikin shekara uku a wannan gwamnati. Dangane da kokarin da hukumarsu ta raya birane da karkara da hasken lantarki ke yi wajen ganin an shawo kan matsalolin da ake yawaitar samu kan lalacewar hanyoyin wutar lantarki ga masu amfani da ita kuwa, babban manajan na REB ya ce, “A gaskiya kan wannan matsala a yanzu kam Alhamdulillah! domin kuwa kan wannan matsalar muna da kwararru da suke aiki ba dare ba rana wajen duba irin wadannan matsalolin, kuma da muka duba wannan matsalar, na daya ma mun hana amfani da turaku na katako.

Kuma akwai wasu unguwanni musamman a Damaturu, wadanda aka sanya wutar lantarki a da can, ko in ce an yi ayyukan cikin gaggawa a lokacin da aka samu sabuwar jiha, watau wurare daban-daban na ma’aikatu da rukunan gidaje irin su; 3-Bedroom na hanyar Potiskum da Gashu’a, Ali Marami, Sani Daura Ahmed da makamantansu, daga baya muka yi nazarin canza su baki daya, muka sanya sababbin turaku.

Haka abin yake a wasu manyan garuruwa irin su Nguru, Yadin-Buni, Geidam da sauransu. kuma a kullum muna bai wa mutane da ma’aikatu shawara duk lokacin da za su saka kayan wuta, su saka masu inganci domin kauce wa faruwar matsalolin da dauke wutar ke haifarwa.

Alal hakika mun cim ma muhimmiyar nasara da muka samu a wannan fannin, sannan a da muna da layin wutar lantarki mai nauyin 132kb a Potiskum, wanda ya rarraba wutar zuwa sauran sassa. Inda daga baya aka samar da wata babbar tasha mai karfin 330kb a Damaturu, wanda hakan ya raba jihar Yobe bangarori biyu.

Ta hanyar Potiskum shi ne zai je Nangere, Jakusko har Gashu’a zuwa Yusufari ya dawo Fika har zuwa KukarGadu. Shi kuma na Damaturu shi ne ya dauka zuwa Gulani, YadinBuni, ya nausa Babbangida, Dapchi, Yunusari, Geidam da sauran garuruwa da kauyukan da ke kan layin.

Bayan wannan tsarin, gwamnatin jihar Yobe ta yi wani tsari na musamman wanda zai sanya ido wajen tabbacin wutar ya kai duk inda ake so, shi ne akwai wasu layukan raba wutar lantarki wanda ake kira 33kb, wanda su ne suke daukar wutar zuwa manyan garuruwa, kuma dukkanin layukan sababbi muka saka.

Sannan mun saka ido duk inda aka sami wata matsala daga Damaturu zuwa Potiskum, daga Potiskum zuwa Gashu’a, haka daga Damaturu zuwa Dapchi zuwa Bayamari komai kankantar matsalar, nan take za mu dauki matakin gyara.

Haka nan a kullum ma’aikatanmu suna bibiyar duk inda suka hango wata matsala ta taso nan da nan sai an gyara ta, a duk yadda take kuwa. Wannan ya sa ne suka jawo za ka ga ana samun hasken wutar lantarki a kowane lokaci a jihar Yobe, musamman manyan garuruwan da muke da su”.

Ganin wannan hukuma tana karkashin ma’aikatar sufuri da makamashi, ko akwai matsalolin da kuke fuskanta? Har ila yau, lura da kan cewar wannan hukuma na karkashin ma’aikatar kula da sufuri da makamashi ya sa tun kafa wannan hukuma ta raya yankunan karkara da wutar lantarki (REB) ba ta taba zaman kanta ba, kowane lokaci takan kasance ne a karkashin wata ma’aikata, ka ga kenan mun saba gudanar da ayyukanmu wuri guda, kuma muna aiki a matsayin uwa da ‘ya, sannan ba mu kadai ne a karkashinta ba, akwai hukumar kula da motocin sufuri ta Jiha (Yobe Line) da hukumar kula da dokokin hanya da masu amfani da hanyar ta Jiha (YOROTA) sai kuma hukumar kula da filin jirgin sama na kasa da kasa na Muhammadu Buhari Cargo International Airport wadda dukkanin nasarorin da muke samu muna samu ne da taimakon Allah da kuma goyon baya da muke samu daga wajen gwamna Mai Mala Buni.

Har ila yau, wannan hukuma ita take kula da ayyukan samar da wutar lantarki a dukanin asibitocinmu a jihar Yobe. Wanda sun hada da asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe, asibitin kwararru, asibitin kula da lafiyar mata na Janar Sani Abacha, tare da asibitocin kwararru da ke garuruwan Potiskum, Geidam da kuma Gashu’a.

Don haka, gwamna Buni na ba mu goyon baya domin ganin ayyukanmu na gudana dari bisa dari”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *