Yunkurin tsige Mahadi: Majalisar zamfara ta kare kanta

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta bayyana dalilinta na yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Barista Mahadi Aliyu Gusau, inda ta ce, tushensa zargin almundahana.

Da yake zantawa da manema labarai a fadar majalisar dokokin jihar, shugaban kwamitin kula da harkokin yada labarai na majalisar, Alhaji Shamsudeen Hassan Bosko ya ce, sun cika sharudan sashe na 188 na Ya ce “Mataimakin gwamna Mahadi Aliyu Muhammad Gusau ya kai kara wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin cewa, majalisar na shirin tsige shi”.

Ya ce, kotun ta bayar da umarnin kiyaye dokokin da bangarorin biyu suka yi kan lamarin, kuma “Wannan ya bai wa mataimakin gwamna Barista Mahadi Aliyu Gusau dama ya yi dukkan ayyukan mataimakin gwamna a jihar ba tare da mutunta gayyatar majalisar ba”.

Ya bayyana cewa, majalisar ta yi biyayya ga umarnin kotu da aka samu, bisa umarnin da ke da takamamman ka’idar kwanaki.

Ya ce, cikin zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwamnan sun hada da “Karya kundin tsarin mulki na sashe na 190 da na 193 (1), (2) (a) (b) (c), na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara).

Kokarin azurta kai da aikata laifuffuka ta hanyar amfani da kudaden jama’a, wannan ya hada da karkatar da asusun gwamnati da laifin zamba da hada baki da kuma amincewa da yin murabus na rashin tabbas a ofishinsa.

“Ya kamata jama’ar jihar Zamfara su sani, Majalisar Dokokin jihar Zamfara mai zaman kanta ce, ba ta bayar da kwangila ko aiwatar da ayyuka ba, sai dai tana gudanar da ayyukan sai do a tsarin mulkin kasa kamar yadda dokokin Nijeriya suka tanadakundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara) wanda ya bukaci kashi 2/3 na daukacin ‘yan majalisar su amince da sanarwar tsige shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *