Yusuf Abba Sarki ya ce: Khalil zai inganta rayuwar al’umma, muddin…

Rikicin Malaman Kano: Imam Alhamidi ya yi gum

Sheikh Ibrahim Khalil

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Wani magoyin bayan Malam Ibrahim Kalil, malam Yusuf Abba Sarki ya bayyana cewa, takarar Malam Ibrahim Khalil a matsayin gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar ADC takara ce da aka shogo ta domin inganta rayuwar al’ummar jihar Kano idan Allah ya bai wa Malamin Nasara ya zama gwamnan jihar Kano.

Sarki ya bayyana hakan ne a toron mika fom da kaddamar da takarar Malam Ibrahim Khalil a matsayin gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar ADC, wanda aka gudanar a dakin taro da ke gidan Mumbayya, Kano, a makon nan.

Ya kara da cewa, a halin da muke ciki, lallai malamai sai sun tsunduma sosai a harkar siyasa, sabanin abin da al’umma da sauran ‘yan siyasa suke zatan cewa, malamai ba za su yi siyasa ba.

“Muna so mu canja tunanin mutane da suke cewa, wai siyasa cin mutunci ce ko karya ce ko yaudara ko wata harka ce ta mutane marasa daraja. Muna so mutane su sani cewa, siyasa ta mutanen kirki ce, ta malamai, ta mutanan da suka san ya kamata” a cewarsa.

Ya kara da cewa, abin da suka sa a gaba a yakin neman zabensu su ne, samar wa al’umma ingantaccen ilimi da gina tattalin arzikin jihar wajen ganin sunanta da aka sani tun a da na cibiyar kasuwanci ta Afirika ta yamma ya dawo da inganta harkar noma da kiwo da kuma inganta harkar lafiya.

“Kowa ya san gwaninmu babban manomi ne kuma dan kasuwa ne kuma jajirtacce ne, saboda haka ta kowane fanni zai yi amfani da kwarewarsa wajen ganin ya dabbaka wadannan kwarewar wajen ganin ya dabbakata a jihar Kano domin samun ci gaba”.

A bangaren kiwon lafiya da gyara mahalli, Yusuf Sarki ya ce, idan Allah ya bai wa gwaninsa nasara zai yi kokari wajen ganin an inganta harkar lafiya ta yadda za a samar da kwararrun likitoci da kayan aiki a asibitocinmu, ta yadda mutane za su daina zuwa asibitocin kasashen waje dominneman magani.

A bangaren inganta mahalli, ya ce, suna so jihar Kano da zama abar musali wajen tsafta da kuma inganta muhalli, inda za su zo da sababbin tsari domin tsabtace jihar da kuma inganta tsarin gine-gine.

Da ya juya kan kalubalen da ke tsakaninsu da manyan jam’iyyun da ke neman gwamnan Kano, Sarki ya ce, musalai sun faru a lokutan siyasun baya, inda ya bayyana cewa, “lokacin da Malam Ibrahim Shekarau ya yi takara a shekarar 2003, mutane har dariya suka dinga yi, amma da Allah ya tashi ikonsa sai ga shi Malam ya zama gwamna har karo biyu.

Duk wata tafiya idan ka ga ana kaskantar da ita to wannan shi ne alamun samun nasarar tafiyar” Daga karshe ya ce, tafiyar Yusuf Abba ba bukatar Malam Ibrahim Khalil ba ce, su ne al’ummar Kano suka ga dacewarsa na ya jagorance su, ganin sun gaji da ‘yan siyayar da suke bata siyasar Kano da cin zarafin mutane da sunan siyaysa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *