Za a bude kasuwar albasa ta duniya -Domin tunawa da Sidi Sakkwato

Gwammna Tambuwal

Tura wannan Sakon

Musa Lemu Daga Sakkwato

Kasuwar albasa za ta hada gwiwa da kungiyar dillalan albasa ta kasa domin bude katafariyar kasuwar du­niya a Sakkwato da aka yi wa lakabi da SIDI ONION INTERNATIONAL MAR­KET SOKOTO.

A lokacin da yake zan­tawa da manema labarai a Sakkwato a ranar Litinin da ta gabata daya daga cikin ‘ya’yan Marigayin Sidi Sakkwato, Alhaji Sa idu Sidi ya ce, zuri’ar Marigay­in sun tsayar da shawarar ne domin taimaka wa jama’ar jihar tare da rage cinkoson al’umma wajen saye da sayar wa.

Babbar kasuwar mai shaguna fiye da 2000 da zai samar da ma’aikata fiyea da 6000 da ya shafi duk­kan kananan hukumomi 23 da ke cikin jihar a inda za a cim ma nasarar rage zaman kashe wando ga matasa.

Alhaji Sa idu Sidi ya ce, tuni aka yi tanadin ofis-ofis na ma’aikatan kashe gobara dana tsaro tare da sanya na’ura domin karfafa matakan tsaro.

Kasuwar za ta zama daya daga cikin manyan ka­suwanni a kasar nan da aka kashe miliyoyin kudi domin kara inganta tattalin arziki da habaka kasuwanci, inda aikin ginin ya kankama da ake sa ran bude kasuwar watanni biyu masu zuwa.

Sa’idu Sidi Sakkwato ya ce, tuni gwamnatin ji­har Sakkwato a karkashin gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta yi na’am tare da nuna goyon baya a inda ya ce, kasuwar za ta samar da ayyukan yi ga matasa da inganta tattalin arziki kamar yadda gwamna Tambuwal ya bayyana in ji Sa’idu.

Daga karshe ya ce, an tsara kasuwar ta yadda za a kawar da dukkan mat­salar cinkoso ga manya da kananan motoci da sauran dukkan ababen hawa ganin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *