Za a fassara hudubar Arafa cikin harsuna 10- ciki har da harshen Hausa

Tura wannan Sakon

Fassarar Aliyu Umar.

Mahukunta a kasar Makka sun ce,a yayin Hajjin bana 1443(2022)za a fassara hudubar filin Arafa zuwa manyan harsuna 10 na duniya, nan take.

Wannan yana kunshe ne cikin wani bayanin sakon da ya fito daga hadiman Masallatai masu alfarma ta yanar gizo.

Harsunan 10 sun hada da Turancin Ingilishi da Malesiya da Urdu da Farisa( Iran) da Turancin Faranshi da kuma Sin(China).

Sauran su ne harsunan Turkiyya da Rasha da Hausa da kuma Bengali. Ana yin hudubar aikin Hajjin a ranar hawan Arafa,9 ga Zul-Hijja kenan kuma hawan Arafan rukuni ne na hudu a jerin rukunan Hajji hudu,sauran su ne (1) Yin harama da aikin Hajji( dayan nau’i uku) (2) Dawafin Ifada(3) Tattaki tsakanin Safa da Marwa(4) Hawan Arafa.

Kuma a filin Arafa ake dakatawa tun daga fitowar rana zuwa faduwarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *