Za mu bai wa Sanatan Kano ta tsakiya goyon baya -Ahmad Gadan

Daga Ibrahim Muhammad Kano
Za mu bai wa dan takarar majalisar dattawa na Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP, Dokta Abubakar Nuhu Danburam goyon baya domin kai wa ga nasara.
Dan jam’iyyar PDP a yankin karamar hukumar Gezawa, Ahmad Gadan ya bayyana haka da yake zantawa da ‘yan jarida. Ya ce, a wannan lokaci da za a tunkari zabe na 2023 tsayar da mutane masu kima da nagarta irinsu Abubakar Nuhu Danburan da aka yi zai taimaka wa nasarar dan takararsu na shugaban kasa Atiku Abubakar.
Malam Ahmad Gadan Gezawa ya ce, a lokacinda Dokta Abubakar Nuhu ya yi kwamishina a jihar Kano ya zo da abubuwa da dama na habaka ci gaban al’ummar jihar Kano, suna ji sun kuma gani a kasa irin kyakkyawan shaidar da al’ummar karamar hukumar Birnin Kano suke yi masa a lokacin da ya wakilcesu a majalisar tarayya.
Saboda haka suna da da kyakkyawan fata a kansa na takara da ya samu na Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar PDP kuma kasancewar karamar hukumar Gezawa na cikin yankin mazabar Kano ta tsakiya za su ba shi cikakken goyon baya da zai kai ga nasara da yardar Allah. Ahmad Gadan ya ce, PDP tana kara samun karbu
a tsakanin al’ummar jihar Kano, sanin irin kyakykyawawan manufofinta da suka mora kafin a zo a yi masu dadin bakin zabar wannan gwamnati ta yanzu suke dana sani saboda mawuyacin kuncin rayuwa da fargaba da ta jefa al’umma musamman talakawa