Za mu bude madatsar Tiga cikin Yuni –Gawuna

Za mu bude madatsar Tiga cikin Yuni –Gawuna

Alhaji Nasiru Yusif Gawuna,

Tura wannan Sakon

Rabiu Sunusi Katsina

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Nasiru Yusif Gawuna, ya tabbatar da cewa, zuwa nan wata biyar gwamnati za ta sake bude Dam din Tiga da ke karamar hukumar Dawakin Kudu.


Bukatar hakan ya biyo bayan korafe korafen da manoman rani suke bayyanawa a yankunan karamar hukumar Dawakin Kudu dama makwabtan ta da gyaran Dam din ya zama kalubale gare su domin sun samu tsaikon ayyukansu na wannan lokaci.

Gawuna wanda shi ne Kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar, ya bayyana haka a wajen taron baje kolin ayyukan ma’aikatar noma da albarkatu kasa na jihar Kano ga manema.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa, bukatar gyaran Dam din yana da nasaba da yunkurin gwamnati tarayya na kula da DamDam da ke karkashin kulawar ofishinta na (HADEJA JAMA’ARE) domin tabbatar da bunkasar harkokin noman Rani a yankunan.

Nasiru Yusif Gawuna ya kuma kara da cewa “Mun tsaida harkokin noman Rani da mazauna yankin suke yi ne domin yashe dam din, amma ba mu muke da alhakin yin hakan ba, akwai wakilan gwamnati tarayya da ke kula da harkoki damadaman Hadeja da Jama’are, kuma su suke kula da aikin ba gwamnatin jihar kano ba”in ji shi.

“Atsawon shekarun nan an samu tsaikon gudanar da aikin ne sakamakon daga hukumar da ke kira hukumar kula da koyar da dabarun noman rani da ke kasar nan” Saboda haka dole mu bar su su gudanar da aikinsu, domin ba za su iya yin aikin lokacin da ruwa ke cikin dam din ba, Domin haka zai iya haifar da matsalar ambaliyar ruwa ba ga manoma ba kadai har ma da gidajen al’ummar yankin. “Amma ya zuwa yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *