Za mu ci gaba da gudanar da ayyukan alheri -In ji Tambai Kwa

Tambai Kwa

Tambai Kwa

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan, Kano

Shugaban majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai Kwa ya ce, karamar hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan alheri a fadin yankin ta yadda al’ummar karamar hukumar za su amfana da ribar dimokuradiyya bisa jagorancinsa.

Ya yi tsokacin ne a wata ganawa da ya yi da wakilinmu, dangane da cikarsa shekara daya kuma a karo na biyu bisa shugabancin karamar hukumar Dawakin Tofa, tare da jaddada cewa, da yardar Allah, kowace mazaba za ta rabauta da muhimmin aiki domin kyautata zamantakewar al’umma.

Alhaji Ado Tambai Kwa ya kara da cewa, sanin kowane cewa, majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa tana kokari sosai wajen samar da romon dimokuradiyya a kowane sako da lungu na yankin, sannan ana taba kowane fanni a aikace, domin haka za su kara himma wajen ganin ana ci gaba da amfana da shugabancinsu.

Dangane da irin nasarorin da suka samu, Ado Tambai Kwa ya sanar da cewa, suna kokari kan harkar ilimi wanda shi ne ginshikin rayuwar al’umma suna bai wa mata da matasa kulawa wajen samar masu da hanyoyin dogaro da kai da bayar da horo kan sana’oi da kuma kyautata harkokin kula da lafiya ba tare da nuna gajiyawa ba.

Haka kuma shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa, yanzu haka suna kara yin kokari wajen kara bullo da sahihan hanyoyi na inganta zamantakewar al’umma ta fuskar tsaro da kuma tabbatar da cewa, ana bin doka da oda a fadin yankin.

Ya yi amfani da wannan dama inda ya jinjina wa gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da yake yi wajen kawo managarcin ci gaba a jihar Kano, tare da kyautata tsarin tafiyar da siyasa a jihar da kuma inganta dangantaka tsakanin gwamnatinsa da majalisun kananan hukumomi wanda hakan ya taimaka wajen tafiyar da jagorancin al’umma cikin nasara.

A karshe, Alhaji Ado Tambai Kwa ya gode wa daukacin al’ummar karamar hukumar Dawakin Tofa, saboda kaunar da suke nuna masa ba tare da nuna gajiyawa ba, sannan ya yaba wa ‘yan majalisar dokoki da na zartaswa na karamar hukumar bisa yadda ake tafiya tare kuma ake aikin al’umma ba tare da wata matsala ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *