Za mu ja damarar yaki da almundahana -Kauran Bauchi

Idan masalaha ta gagara, ba na tsoron bugawa da kowa -Bala Mohammed

Bala Mohammed

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau daga Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya ce, gwamnatin sa ba za ta lamunci rashawa ba a matakin jiha da kananan hukumomi ba.

Gwamnan ya bayyana hakan yayin sanya hannun kan dokar kirkiro hukumar saurare da karbar koke-koken al’umma kan cin hanci da rashawa a fadar gwamnatin jihar. Kirkiro hukumar a cewar gwamnan na daga cikin shirin gwamnatin za na cin moriyar tsarin kasa na fadada dokoki ga jihohi kamar yadda yake kunshe cikin daftarin dokokin Nijeriya.

Ya kara da cewa, samar da hukumar la shakka zai taimaka wajen kula da lamuran cikin gida da suka hada da inganta tsaro da bincike da gurfanarwa la’akari da al’adun al’umma.

Gwamna Bala ya ce, hukumar za kuma ta samar da guraben aiki ga dimbin matasa sanya wa dokar hannu ta shiga cikin tarihin hobbasar gwamnatinsa na tabbatar da adalci da bin bahasi. Tun farko da yake jawabi, kakakin majalisar dokoki ta jiha, rAbubakar Y. Suleiman da ya samu wakilcin mataimakin sa Danlami Kawule, yaba wa hadin kan da ke tsakanin zababbu da fannin zartarwa ya yi tare da kira ga daukacin al’umma da su ci gaba da mara wa gwamnatin baya.

Bikin sanyawa dokar hannu ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyar PDP matakin jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *