Za mu kawo ci gaba a Dambatta, Makoda -Dokta Wailare

Dokta Wailare

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Dan takarar majalisar wakilai daga mazabar tarayya ta Dambatta da Makoda, Dokta Saleh Musa Wailare ya ce, zai yi kokari wajen samar da ci gaba a kananan hukumomin Dambatta da Makoda idan aka zabe shi a matsayin wakilin mazabar a zaben 2023.

Dokta Wailare wanda shi ne dan takarar kujerar wakilcin mazabar tarayya ta Dambatta da Makoda a PDP ya yi bayani ne a hirar su da wakilinmu a Kano, inda ya sanar da cewa, yana da manufofi kyawawa na bunkasa zamantakewa al’ummar yankin idan Allah ya ba shi nasara a zaben da za a gudanar na 2023.

Ya nunar da cewa, dimokuradiyya a Nijeriya tana bukatar mutane masu kwazon kawo abubuwa masu amfani ga al’umma bisa la’akari da bukatun su da guraren da suke zaune ta yadda rayuwar su za ta ci gaba da kasancewa cikinyanayi mai kyau.

Haka kuma ya jaddada cewa, aikin ‘yan majalisa shi ne yin dokoki wadanda za su zamo jagora a zamantakewa da mu’amulla ta al’umma bisa sanin ya kamata da zaman lafiya, sannan akwai bukatun al’umma wadanda ake gabatarwa a zauren majalisa domin shigarwa cikin jadawalin aiwatar wa daga bangaren gwamnati.

Dangane da yadda ya ga irin shirye-shiryen da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ke yi na tunkarar zaben 2023, Wailare ya nuna gamsuwar sa bisa tsare-tsare

kuma gargadi ‘yan siyasar kasar nan da su guji yin amfani da matasa wajen haddasa rikice-rikice yayin yakin neman zabe da kuma bayan zabe ta yadda kasarnan za ta ci gaba da zamowa a sahun gaba ta fuskar dimokuradiyya da kuma siyasa mai tsafta, inda kuma ya shawarci matasan da kada su yadda a yi amfani da su wajen tayar da hargitsi domin biyan bukatun wadansu marasa kishin kasa.

A karshe, ya yi amfani da wannan dama wajen yin godiya ta musamman ga daukacin al’umomi Dambatta da Makoda maza da mata saboda goyon bayan da suke ba shi tun da ya amsa kiran da suka yi masa na ya fito wannan takara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *