Za mu kwato wa kanawa hakkinsu bangaren noman dawa -Badamasi Bunkure

Za mu kwato wa kanawa hakkinsu bangaren noman dawa

Noman Dawa

Tura wannan Sakon

Labari Rabiu Sunusi daga Katsina

Kungiyar manoman dawa ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana sabon shirinta na mayar da martabar noman dawa a jihar Kano.

Hakan ya fitodaga bakin shugaban kungiyar na jihar, Malam Badamasi Bunkure a wata zantawa da Albishir makon da ya gabata.

Bunkure ya bayyana cewa, lallai su ya zuwa yanzu sun dauki aniyar kawo gyara ga kungiyar manoma dawa a jihar shi domin cin gajiyar noman ga al’ummar su.

Bunkure ya ce, batun matsalolin da suka faru kafin karbar shugabancinsu kuwa lallai ba za su sa ido ga wadanda sukai wa manoman dawa na jihar Kano lumbu-lumbu ba.

Shugaban ya ce, sun amsa kiran manoman ne domin zuwa da kawo gyara da wadansu shugabanni da ba ‘yan asalin jihar Kano ba sukai wa manoman dawar ba tare da lakume abin da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar, domin gudanar da noman.

Sannan ya tabbatar da cewa, zuwansu kujerunsu sai da shugaban kungiya ta kasa, Alhaji Baba Yamaina ya ja masu kunne cewa, duk rintsi aikinsu ya kai ga talakawan da suka amsa sunansu talakawa ba masu riga da sitati ba.

Sannna ya bayanna cewa, lallai shi manomin da aka taimakama wa ana so idan an taimaka masa ya noma abincin da zai ci har ma ya sayar a kasuwa, domin wadansu su amfana wannan shi ne tsarin kungiyar manoman dawa ta kasa, kuma shi aka karantar da su matsayinsu na shugabannin jihohi.

Haka Kuma ya bayyana jan hankalinsa ga jama’ar Arewa da kasa baki daya da su dage wajen maya da hankali kan noman dawa, wanda ya zuwa yanzu ya fara ja baya tare da niyyar shudewa ma.

Kazalika ya kuma bayyana kudurin shugaban kasa Muhammadu Buhari na inganta noma da kiwo a ka- Za mu kwato wa kanawa hakkinsu bangaren noman dawa -Badamasi Bunkure sar nan ya kara masu kwarin gwuiwa wajen tsayuwar daka tare da farfado da noman dawa a jihar Kano.

Kuma ya tabbatar da cewa, ya zuwa yanzu sun samu nasara kan noman dawa a jihar Kano sabanin baya da kusan noman shinkafa ya fara danneta, amma cikin hikimar Allah ana samun canji daga manoman, ta hanyar kayan aiki da suka dauki alkawarin bai wa manoman tare da tallafin daya dace daga gwamnati.

Badamasi Bunkure ya kara da cewa, a yanzu manoman ana bukatar su noma dawar ne kawai ake bukata ba wani abuba, wanda idan kudin suke so to za a ba su kudin idan kuma dawarsu suke so to za su dauka.

Bunkure ya ce, sun yi wa matasa shiri na musamman wajen koyar da su dabarun noman dawa tare da hana su zaman banza, sai kuma wadansu yankunan da kasar su ba ta noma dawa suma suna yi masu shirin su na musamman. Badamasi ya kuma bukaci gwamnati jihar Kano da ta taimaka wajen sama wa sassan da kasarsu ba ta noman damina da dama-daman da za su samu ci gajiyar noman dawa da gwamnati tarayya take tallafawar samar da abinci ga al’umma dama kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *