Za mu mayar da Kano kasaitacciyar alkarya -Sadik Wali, Dambatta

Sadik Wali da Dambatta
Daga Rabiu Sunusi,
Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin tutar jam’iyyar PDP, Sadik Wali da mataimakinsa tsohon kwamishinan kasa da tsara birane na jihar Kano, Alhaji Yusuf Danbatta sun bayyana aniyarsu ta sauya fasalin jihar Kano ta kowace fuska idan Allah ya ba su aron alkyabbar mulkinsa a zabe mai zuwa na shekarar 2023.
‘Yan takarar sun tabbatar wa wakilin Albishir hakan a wata ziyara da suka kai wa Alhaji Yahaya Bagobiri wanda shi ne shugaban tafiyar dan takarar shugaban kasar Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, domin nuna matukar godiyarsu musamman tafuskar kokarinsa da yake na ganin PDP ta samu nasarar a jihar Kano dama kasa baki daya.
Sadik Wali ya kuma bayyana matsayin Bagobiri uba ne a garesu domin haka ya ga dacewar kawo mashi wannan ziyara ta musamman domin tattauna irin abubuwan da ke faruwa ta hanyar daya da ce ganin samun nasarar da suka yi a kotu yayin da bayyana su a masu nasarar samun tikitin tsayawa takarar gwamnan jihar Kano da mataimakinsa Danbatta.
Ya ce, ya zuwa yanzu al’ummar jihar Kano ba su bukatar zayyano masu irin matsalolin da jam’iyya mai mulki yanzu ta ingiza da yawan jama’a cikin halin kakani kayi, domin haka ya zama izina garesu da su zabi PDP domin mayar da martabat jihar a idon duniya.
Shi ma Dantakarar mataimakin gwamnan kuma tsohon kwamishinan kasafin kudi a jihar, Alhaji Yusuf Bello Danbatta ya ce, sanin kowane yadda suka gudanar ma jihar Kano ayyukan dimukuradiyya a lokacin dasuke mulkinsu a tsohuwar gwamnati lallai abin a yaba ne, domin haka ne ya ga dacewar tsayawarsu takara tare da dorawa daga inda ya kamata.
Danbatta ya kuma bayar da misali da shi Dantakarar gwamnan watau Sadik Aminu Wali matsayin masani a harkar ruwan sha tun da har ya rike matsayin kwamishinan ma’aikatar ruwan famfo to lallai idan Allah ya ba su damar cin zabe kallon da ake yi wa jihar Kano na matsalolin ruwa zai zama tarihi.
Bayan batun ruwakuma akwai bangarori na ilimi da harkar tsaro da noma da kiwo da uwa uba sashen kiwon lafiya da sauran abubuwan da za’a samu nasarar mayar da jihar Kano zakaran gwajin dafi a kasar na musamman jihar Kano da take karbar kambun ragamar cibiyar kasuwanci a idon duniya, in ji Danbatta.
Shi ma da yake jawabi maimakon Alhaji Yahaya Umar Bagobiri daraktan magoya bayan masoya Wazirin Adamawa, Alhaji Kabir Abdulkadir Jibrin da aka fi sani da “Dan Kurna” ya ce, dama tun da aka yi zabe suke jira suga wane ne dan takarar da INEC za ta bayyana matsayin wanda ya ci zabe kuma Allah ya ba shi nasara kaga yana da kyau su zo domin tabbatar da hadin kai da goyon bayan da ya kamata a ce an yi matsayin jam’iyya daya kuma komi daya da kuma tunanin yadda za’a samu nasarar cin zabe daga sama har kasa a zabe mai zuwa insha Allah.
Dan-kurna ya nuna godiya ga Allah sakamakon lokutan baya su ne suke daga waya su kira jama’a zuwa tafiyar Atiku Abubakar, amma ya ce , ya zuwa yanzu a kullum jama’a ne ke nemansu domin hadakar goyon baya tare da nuna sha’awarsu wajen tafiyar Atiku a zabe mai zuwa shi suke da bukatar ya ci zabe.
“A yanzu duniya ta waye ga bangaren siyasa hakazalika Nijeriya da jihar Kano ma ba a barsu a baya ba ta fuskar fahimtar wanda zai kawo masu ci gaba domin haka al’umma shi za su yi a Kano, in ji shi.