Za mu wadata manoman Nijeriya da taki -In ji Alhaji Rabi’u Muhammad

Tura wannan Sakon

Tun daga lokacin da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta tsame han­nun ta gaba daya a duk wani batu na samar da takin zamani ga manoma da suke sassan kasar, manoman suka shiga matsaloli da dama, kama daga rashin taki yalwatacce a hannunsu da tsadar takin da kuma yadda wasu ke amfani da damar da suka samu, su na shigo da takin Nijeriya da ke cutar da manoma a wasu lokuta ma, sai ka ga ana samun takin da ake cakuda shi da yashi ko kasa da dai sauran matsaloli da dama da manoman ke fuskanta.

Domin samun fitar matsalolin da manoma ke fuskanta, wakilinmu da ke Zariya ISA A. ADAMUya sami damar tattaunawa da babban darakta a cibiyar binciken sinadirai a bangaren tsare – tsaren da aka fi sani da ‘’ NATIONAL RESEARCH INSITUTE FOR CHEMI­CAL TECHNOLOGY’’ da ke Zariya mai suna ALHAJI RABI’U HALIDU MUHAMMAD, inda ya warware zare – da – abawa kan yadda cibiyarsu ke samar da takin zamani da zama mai am­fani ga ko wace jiha a tarayyar Nijeriya a shekaru fiye da ashirin da suka gabata.

Ga dai yadda tattaunawarsu ta ka­sance da wakilinnamu,

— Ina aka tsaya a ayyukan da wan­nan cibiya ke gudanarwa na samar da takin zamani ga manoman Nijeriya da ku ka fara shekaru da dama da suka ga­bata ?

— Kafin in fara yi ma ka bayanin inda aka tsaya a batun samar da takin zamsni mai inganci da wannan cibiya da ake kira [ NARICT ] a takaice, zan bayyana ma ka cewar, tun farko an kafa wannan cibiyar ce domin yin bincike da ya shafi jama’armu baki daya da ya shafi bincike, musamman al’amarin da ya shafi takin zamani ga manoma da suke sassan Nijeriya.Domin mafiya takin zamanin da mu ke samu ko ake shigo da su daga waje, su na da babban illa ga kasa ga kuma illa ga amfanin go­nar da aka sa wa takin zamanin.

Kamar shi wannan takin zamani da ake kawo Nijeriya daga kasashen waje, in ka kammala noman da ka yi aka dauki amfanin gonar zuwa kasashen waje, ba za su yadda a shiga da amfanin gonar kasarsu ba, domin za su ce an yi amfani da wani kirin sinadarin wajen yin takin da ke cutar da rayuwar dan adam, kuma ko da kasashen duniya ka je, musamman in ka ziyarci shagunan sayar da abinci da kayayyan ruwa, kamar su timatir da sauransu, za ka cimma inda aka aje kay­ayyakin daban -0 daban ne, wato wabda aka yi amfani da wancan sinadarin da ke cutar da al’umma daban da kuma wanda ko da mutum ya ci bai zai yi ma sa komi ba, shi ma daban, kuma takin da aka yi noman da wanda bay a cutarwa daban yak e, domin su sun san ba ya cutar da dan adam, zuwa yanzu ma.turawa ma su na gudun duk wani kayayyakin abincida aka hyi da wancan sinadarin da ke cutar da al’umma.

— Ya turawa su kan su su ke daukar takin da ake yi a kasashensu wanda ake shigo da su Nijeriya ?

— Ai bincike ya tabbatar da cewar, su kan su turawa na gudun takin zama­nin da aka yi da sinadarin da ake kira ‘’ CHEMICAL PERTILIZER’’ Amma wanda aka yi da ‘’ORGANIC PERTIL­IZER’’ shi su ke so, shi ne kuma su ke runguma da hannu biyu, kuma duk no­man da aka yi da ‘’ORGANIC PERTIL­IZER, abin da aka shuka ya fi wanda aka shuka da ‘’ CHEMICAL PERTIL­IZER’’ tsada da kuma runguma hannu biyu ga kasashen duniya.

—- To ku wanne ku ke yi a cikin taki guda biyun da ka bayyana ma na abaya ?

To, a gaskiya cibiyarmu [ NARICT ]mun fi mayar da hankali da yin takin ‘’ ORGANIC PERTILIZER ‘ , kuma shi ne mu ka yi su na da kuma fice a kansa a sassan Nijeriya da wasu sassa na du­niya, kuma a kwai kwararrun ma’aikata da mu ked a su da suka yi fice wajen gudanar da bincike a wannan fagen na samar da wannan taki da na bayyana ma ka a baya da kuma na ce ma ka kasashen turawa ma, shi suka fi so, saboda dalilan da na bayyana ma ka a baya.

—– To, da wasu sinadirai ku ke am­fani das u, wajen yin wannan takin da ka ambata cewar shi cibiyarku ke yi a shekaru da dama da suka gabata ?

—- Kafin mu fara yin takin, said a mu ka gudanar da bincike, inda mu ka gano amfani da itaciyar da ake kira DOGON YARO, wato ‘ya’yan itaciyar, wato NIF, kuma mun fara hulda da wasu jihohin da suke arewa da kuma wasu ji­hohi a sassan Nijeriya, musamman a kwai jihohi uku a arewacin Nijeriya da kuma jihar guda daya a kudancin Nijer­iya, wadannan jihohi su ne Katsina da jihar Kabbi da jihar Anambara da jiharKogi.

—- Wasu alfanu kuma ku ka gano da ku ka fara amfani da wannan itace na Dogon yaro, wato Bedi ?

—- Lallai a kwai abubuwan ci gab­an al’umma da mu ka gano,na farko zai samar wa matasa maza da mata ayyukan yi, ta samo ‘ya’yan dogon yaro, su na kawo ma na, mu na saye a wannan cibi­ya ta [ NARICT ],ka ga sun sami wata hanya da za su sami ‘yan kudin da za su yi amfani da su a wajen hidimominsu nay au da kullun, sai kuma in an kawo ma na cikin wannan cibiya, mu na gurza shi, mu cire man gyada san nan kuma bayan an cire man, abin da ya rage da shi mu ke yin takin zamanin, mu na yin magani sauro, da aka fi sani da shaltos da, ga manoma kuma mun samar ma suwani sinadari da mu ka hada da wan­nan, mu ka sami abin da ke kasha gona­kin manoma, ga maganin sauro, da dai abubuwa da yawan gaske, duk mu na yi da wannan ‘ya’yan itace na Nif, amma dam un sami kwarin gwiwa da babu ko shakka dam un samar da takin zamani mai inganci da manoman Nijeriya za su rika amfani da shi.

Kuma takin ya yi dai – dai da kasar­su, wato ba ya kawo ma su wani lahani a gonakinsu.

—- Zuwa yanzu, ina aka tsaya a tsakanin jihohin da ka bayyana a baya, na yunkurin samar da wannan takin da ka ambata ?

— Za a iya cewar, komi ya tsaya cik, domin duk da mun fara yin takin jihohin da aka ambata duk sun fara amfana, sun kuma ga amfaninsa da alherinnnnsa da manomansu ke bayyana ma su,amma ba a ci gaba da tsarin da mu ka tsaya a tsakaninmu cibiyarmu da jihohin da mu ka bayyana a baya ba, mu na ganin, babu abin da ya kawo tsayawar tsarin sai canjin gwamnatin da ake ta samu daga gwamnatin da mu ka fara magana da su yau., ka san a mafiyawan lokuta

duk gwamnati in ta zo, ta na da Alkiblar da ta ke son ta dosa, in bai yi dai – dai da wadda ta gada ba, sai ta aje abin da gwamnatin da ta gabata ta runguma, ta rungumi na ta, wannan shi ne mu ka fus­kata zuwa yau.

—- Bayan gwamnatocin da ka am­bata sun tsaya kan ci gaba da inda ku ka tsaya, me ku ka yi ?

—- To, ka san halin da gwamnati ta ke a yau, matsalolin kudi su ne kan gaba, in mun yunkura, da wuyak mu kai ga inda mu ke son mu je, domin lalitar­mu ba za ta iya daukar nauyin ayyukan da na bayyana ma ka a baya ba., domin tsarin da kuma binciken na bukatyar kudade sosai, to, kudin dais hi ne bab­bar matsalarmu, amma da an daure an ci ganba, zai samar da ayyukan yi ga jihohi da kuma karin kudin shiga ga gwamnatocin ga kuma uwa – uba kuma da karin bunkasar harkar noma, domin takin da mu ke yi, inganta kasa yak e yi, ba kasha kasa ya ke yi ba, kamar yadda takin da ake shigo das hi daga kasashen waje, kuma amfanin gonar da mu ka samu da wannan takin duk duniya ana karbarsa da hannu biyu, kamar yadda na bayyama ma ka a baya.

—- Yanzu, komi ya tsaya cik ke nan a wannan cibiya, a batun samar da wan­nan takin, a dalilin karancin ma su gidan rana ?

— Ko kadan bab u abin da ya tsaya, domin bangaren samar da takin na nan, kwararrun ma’aikatan su na nan, kun­dayen binciken su na nan, mu da mu ke jagorantar binciken da aiwatar da binciken duk mu na nan, babu abin day a tsayar da mu, sai rashin kudin da na bayyana ma ka, ko da a yau, mu ka sami yalwataccen kudi, ko kuma wata jiha ko kuma jihohi su ka kwankwasa ma na kofa za mu bude, domin ci gaba daga inda mu ka dan dakata., in dai ‘yan ka­suwa da gwamnatocin jihohi su ka zo, ako wane lokaci ma na shirye, domin duk abin da mu ke hada wa domin yin wannan takin, babu abu guda da mu ke shigo da shi daga kasashen waje,duk abubuwan da mu ke amfani da su a nan gida Nijeriya mu ke samu.

— A karshe, ina ganin kamar kun a bukatar samun yalwataccen kudi ke nan daga gwamnatin tarayya da ka iya zama, in ma ba ku sami wata jiha ta zo gareku ba , za ku iya ci gaba da samar da ta­kin da ku ka saw a gaba, domin bunkasa noma ga manoman Nijeriya da kuma sa­mar da ayyukan yi ga dinbinmatasan da suka kammala karatu, amma babu inda za su tsuguna domin ci gaba da samun abin da za su ci a frayuwarsu ?

— Lallai babban bukatun mu ke nan, duk gwamnatin tarayya nab akin kokarin ta wannan cibiya, amma duk da haka, kamar yadda na bayyana abaya ne, in an kara yalwata ma na ma su gi­dan rana, za mu samar da takin da zai wadaci manoman Nijeriya, ba mano­man arewacin Nijeriya kawai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *