Za mu yi wa al’umma wakilci nagari -Saleh Marke

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Dan majalisar dokoki  ta jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Saleh Ahmed Marke yace a matsayin su na wakilan al’umma za su ci gaba da yin wakilci nagari tareda samar da ribar dimokuradiyya a mazabun su ta yadda za’a sami zamantakewa mai kyau.

Ya yi tsokacin ne a ganawar su da wakilin mu, inda kuma ya nunar da cewa, “ aikin dan majalisa shi ne yin dokoki wadanda za su kawo ci gaba da samar da ayyukan raya kasa bisa yin la’akari da bukatun al’uma ta yadda kowane bangare na kasa ko jihohi da yankunan kananan hukumomi za su amfana da aikin gwamnati, domin haka muna kokari wajen tabbatar da cewa, wakilcin da muke yi yana amfanar al’umomin mu”. Inji shi.

Haka kuma Alhaji Saleh Ahmed marke ya yi bayanin cewa, a jihar Kano akwai jituwa da dangantakar aiki mai kyau tsakanin majalisar dokokin jihar da bangaren zartarwa, wanda hakan ta sanya gwamnati mai ci take cimma kyawawan nasarori kamar yadda ake gani a fadin jihar, inda kuma yayi godiya ga al’umma saboda goyon bayan da suke bai wa gwamnati.

Dan majalisa Saleh Marke daga nan sai ya yabawa abokan aikin sa watau yan majalisar dokokin jihar kano bisa hada hannu da akayi ana aiki tare musamman ganin yadda wannan majalisa take da shugabanci mai adalci da sanin ya kamata, tareda godewa gwamna Ganduje saboda kokarin da yake yi wajen gudanar da aiyukan alheri a jihar ta kano batare da nuna kasala ba.

A karshe, Saleh Ahmed marke ya yi amfani da wannan dama wajen yin fatan alheri ga daukacin al’umar karamar hukumar Dawakin Tofa saboda kaunar da suke nuna masa wajen bashi damar yi masu wakilci tareda alwashin ci gaba da samar da romon dimokuradiyya a mazabar tasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *