Zabbabbun shugabanni, a yi ayyukan da za su gamsar -Talban Panshekara

Talban Panshekara
Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana zaben da ‘yan Nijeriya suka yi na sabon shugaban kasa dana gwamnoni cikin lumana da kwanciyar hankali sun yi ne da kyakkywar niyya da zaton samun ci gaba.
Talban Panshekara, Ambassador Isyaku Yahaya ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida.
Ya yi kira ga shugaban kasa da aka zaba da gwamnoni da ‘yan majalisu na tarayya dana jiha da sanatoci su taimaka su yi wa jama’a aiki a matsayinsu na amintattu da aka zaba su tabbatar da inganta tsaro da bunkasa harkar noma da wadatar da man fetur yin hakan zai taimaka wajen inganta rayuwar al’umma.
Ambasada Isyaku Yahaya ya yi nuni da cewa, ‘yan Nijeriya mutane ne masu son zaman lafiya da juriya da hakuri a kan duk abin da ake masa, domin haka shugabanni su yi abin da ya dace.
Suna kyautata zato a kan sabon shugaban kasa Tinubu da aka zaba wanda dan siyasa ne, da ke sauraren kokekoken jama’a kamar yanda ya yi a lokacin yana gwamna a jihar Legas ya kawo masu ci gaba.
Sannan ya ja hankalin shugaban kasar a kan ya jawo duk mutumin da zai taimaka masa wajen kawo ci gaba a gwamnatinsa, ya guji sanya bara gurbi da ba talakawa ne a gabansu ba, sai iyalansu da abin da za su tara masu.
Ya yi nuni da cewa, idan shugaban kasa ya tafi da gwamnatinsa da mutanen kirki tsaro da ilimi da noma da sufuri da kasuwanci ya inganta aka kuma bude kan iyakoki domin shigo da kayayyaki amfanin al’umma, hakan zai jawo baki su shigo su zuba jari kasar ta zama kamar yanda kasashe irin su Sin da Indiya suka zama wajen ci gaba.
Talban Panshekara ya ce, irin kyakkyawan shugabanci da Bola Ahmad Tinubu zai yi shi ne zai ba shi dama nan gaba mutane su sake ba shi dama karo na biyu in sun gamsu da mulkinsa. Da ya juya kan gwamnoni, ya yi kira ga sabon gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Gwamnan Kano, a taimaka wa masu sana’oin hannu -el-Sudani Kabir Yusuf da al’umma suka fito suka yi sahihin zabe suka zabe shi yadda ya kamata ba tare da sun karbi kudi ko taliya da aka yita kokarin ba su ba, suka ki suka zabi ra’ayinsu da ya tabbatar da nasarar Abba saboda yarda da gamsuwa da tsarin Dokta Rabiu Musa Kwankwaso wanda lokacin da ya yi gwamnan Kano ya inganta rayuwar talaka ta kowane fanni.
Ya yi kira ga Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi koyi da irin manufofin Kwankwaso domin inganta rayuwar al’ummar Kano da gyara barna da aka yi a gwamnatin da ta shude na kassara harkar ilimi da kasuwanci da sauran bangarori da aka yi.
Ambasada Isyaku Yahaya ya ja hankalin al’ummar Kano a kan su yi wa sabon gwamna uziri saboda ya sami jihar Kano a yanayi mara dadi an lalata abubuwa, tare da fatan Allah ya yi masa jagoranci ya gyara Kano wajen farfado da ilimi da kasuwanci noma da samar da ruwa da inganta tsaro.
Ambasada Isyaku ya ce, suna farin ciki da matakinda Abba Kabir Yusuf ya dauka na farfado da makarantar gyara tarbiyya ta Kiru da matakin dakile matsalar kwacen waya da ke jawo asarar dukiya da rayuka a Kano.