Zaben 2023: Ba mu babu makahon doki –Imam

Zaben 2023: Ba mu babu makahon doki –Imam

Zaben 2023

Tura wannan Sakon

Daga Abubakar Sulaiman Imam

Ya zama dole mu yi karatun ta nitsu wa Kawu nan mu koba domin komai ba saboda goben mu musamman a kakar zabe mai zuwa na 2023.

Dole mu bambance aya da tsakuwa wajen zaben shuwagabanni na gari domin shekaru hudu ba kwana hudu ba ce. Ba zai yiwu a ce kullum sai dai mu zauna mu yi ta zagin shugabanninmu ba, saboda mu muka zabe su da hannunmu amma ba mu da aikin yi da ya wuce aibata su wanda hakan ba daidai ba ne a tarbiya.

Dole mu dauki mataki wajen gyara domin gyaran a hannun mu yake domin muma wakilan (delegate) kan mune wajen tantance irin shugabannin da ya kamata mu zaba, ba yan handama da baba kere ba. Masu son ciyar da kasa gaba, ba masu ciyar da aljihunsu ba, masu kishin al’umma ba masu kishin ‘ya’yansu ba.

Wadannan abubuwan ya kamata mu duba wajen zaben 2023 ba wai wanda za su sayi kuri’unmu da yan kudi kalilin ba wanda ba za su iya mana maganin komai ba, ko kuma wanda za su rarraba mana omo da sabulu ko Indomie domin mu zabe su.

Kamata ya yi a ce mun wuce karnin a siyasance saboda wayewar mu da iliminmu da kuma hangen nesa yafi karfin a ce har wani makahon dan siyasa ne zai zo ya yi amfani da mu na lokaci kalilan ya kuma watsar da mu kamar yadda suka saba a baya.

Mutumin da ana cewa, ga wuta yana ga maciji saboda baya da wata mafita da zai iya samarwa al’umma saboda shi ma bai taimaki kansa ba balle wani. Kullum sai dai maganan iyayen gidansu saboda su ne idon garin, suke turo su har su zo su jagoranci al’umma ko kuma ma su yi kama daura bayan sun san ba su cancanta ba.

Kadan kenan daga cikin suffofin makafi ‘yan siyasa. Da wannan nake jan hankalin masu ruwa da tsaki da mu ma al’umma da mu yi abin da ya dace wajen gane irin mutanen saboda baza su iya yi mana komai ba, domin ba su yi ba a baya a hasali ma amfani kawai za su yi da mutane domin su biya bukatun su dana iyayen gidan su.

Ya kamata mu gane su domin mu fatattake su a zaben gama gari, sa’an nan mu yi tawassali ga Ubangiji shi zai mana zabi mafi alheri domin rayuwar ta inganta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *