Zaben 2023, ina muka dosa

Isma’il Usman Daga Katsina
Jama’a sun amsa kira a matsayinsu na ‘yan kasa, sun yi katin zabe, sun kuma je wuraren da suka yi rajista sun aiwatar da zabubbukansu.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban karamar hukumar Mani, Yunus Muhammad Sani Bagiwa a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a makon da ya gabata. Bagiwa ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su rama alheri da alheri, kasancewar gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya ba su kulawa ta musamman wajen ayyukan jinkai da kyautata rayuwar talakawa.
Yunus Muhammad Sani Bagiwa, ya jinjina wa hukumar zabe, saboda irin shirin da ta yi na aiwatar da wannan aiki, amma ya yi kara kira gare ta da fatan duk inda aka sami ‘yar matsala ko baraka da a yi kokarin gyara ta kafin zuwan zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha. Ya kuma yi kira ga jama’a da su kara hakuri domin komai mai wucewa ne da izinin Allah, wata rana sai labari.
Ya ce, a wadansu wuraren an sami jinkirin kai kayan aiki shi ya sa ba a sami damar fara zaben da wuri ba, a wasu lokutan kuma, a wadansu wuraren an fuskanci matsala daga na’ura mai daukar hoton fuska ko kuma zanen yatsu, amma cikin ikon Allah an yi an gama lafiya. Shugaban karamar hukumar ta Mani ya tabbatar da irin kulawar da gwamna Aminu Bello Masari yake bai wa talakawa ta fuskar kiwon lafiyarsu da ilimin addini da na zamani da samar da wadacce kuma tsaftataccen ruwa da hanyoyi da bunkasa harkar noman damina da na rani da kula da harkokin kiwo da sauransu.