Zaben 2023: Kwankwaso ya cancanci zama shugaban kasa -Zakiru Kusfa

Kwankwaso

Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga  Zariya

Wani matashin dan siyasa mai suna Alhaji Hamisu Zakiru Kusfa a birnin Zariya da ke jihar Kaduna, ya bayyana babu wanda ke da kishin da iya jagorantar Nijeriya, al’umma kuma su amfana da shugabancinsa sai tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.

Alhaji Hamisu ya ci gaba da cewar, duk cikin wdanda ke neman shugabancin Nijeriya da suke niyyar fafata wa a badi, wato shekara ta 2023, babu wanda ya ke nuna damuwarsaa ga al’ummar Nijeriya marasa karfi, musamman ‘ya’yan talakawa, kamar Kwankwaso, musamman, a cewarsa, in an dubi yadda a shekarun baya, ya dauki nauyin karatun ‘ya’yan talakawa zuwa kasashen waje, inda suka yi karatu a fannonin ilimi daban – daban, ba tare da sisin kwabon iyayen yaran ba.

 Ya kara da cewar, tarihi ba zai manta da Kwankwaso ba, na yadda a shekarun baya ya za ga jihohin da suke kudancin Nijeriya, ya gana da matan da aka kasha ma su mazansu a dalilin wani yamutsi da ya faru, bai bar jihohin ba, kamar yadda Zakiru Kusfa ya ce, sai da ya ba matan tallafin kudade, domin su sami abin da za su ciyar da marayun da aka bar ma su.

Da kuma Alhaji Hamisu Zakiru Kusfa ya juya ga ayyukan ci gaban al’umma da ya aiwatar a lokacin da ya ke gwamnan jihar Kano, a cewarsa, ya aiwatar da ayyukan da suka zama abin koyi ga wasu gwamnonin Nijeriya, ba na arewacin Nijeriya kawai ba.

A kan haka ne Zakiru Kusfa yay i kira ga al’ummar Nijeriya, ba na arewa kawai ba, da su yi karatun ta – natsu, wajen zaben shugaban kasa mai zuwa a badi, kamar yadda ya ce, babu wanda zai iya tunkarar matsalolin Nijeriya kai tsaye, sai Kwankwaso, ‘’ ku aje wadanda in sun sami nasara harkar kasuwancinsu za su fi mayar da hankalinsu a kai, ya yin da wasu kuma, in ji Zakiru, za su ci gaba da rura wutar kabilanci ne a Nijeriya, ba su doshi tsaro da sauran matsaloli da suke yin barazana ga ‘yan Nijeriya da kuma Nijeriyar kanta.

A karshe, Alhaji Hamisu Zakiru Kusfa, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da  su toshe kunnuwarsu daga sauraron wadanda ke kawo batutuwan addini a zaben shekara ta 2023, kamar yadda ya ce, batun da aka kawo ke nan a zaben shekara ta 2015, a yau, kamar yadda ya ce, wadanda suka runguma, su suka fi kowa yin da – na – sani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *