Zaben 2023: Me ya sa matasa suka gaza a siyasar Nijeriya?

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

A duk lokacin da aka yi magana kan matasa a wannan kasa ta mu, na kan kara duba yadda matasanmu suka gaza tabuka komai a siyasar kasar nan tun lokaci mai tsawo.

Kuma kowa ya amince cewa, matasa su ne kashin bayan samar da ci gaba a kowace kasa ta duniya duba da yadda zamani yake canzawa daga lokaci zuwa lokaci kamar yadda ake ciki a duniyarmu ta yau.

Haka kuma tun da Nijeriya ta koma kan tsarin mulkin farar hula watau a 1999, duk dan takarar da zai yi yakin nemen zabe yana gin kirari da matasa, matasa kmma da zarar an ci zabe sai a mayar da matasan daga gefe.

Bugu da kari, ana yi wa matasa kirari da cewa, su ne kan gaba wajen kawo sauyi domin suna da yawa, amma a karshe bayan an kammala zabubbuka sai a rinka yi masu wayo da cewa, za a ba su horo kan sana’oi da jari domin dogaro dakai inda kuma dan abin da za a bayar kankane.

Babbar matsala da matasan kasar nan ke ciki ita ce, sun gaza tabuka wani abin kirki a harkar siyasar Nijeriya, musamman zaben 2023 inda dattawa suka babbake komai su kuwa matasa amfani kawai ake yi da su domin cim ma bukatu na siyasa da kuma mulki kamar dai yadda ake gani a yau. Abin takaici shi ne, matasan mu sun kware wajen kakkafa kungiyoyin tallar ‘yan takara domin samun abin duniya, wadansu kuma sun kware wajen tayar da hargitsi lokutan zabe da sacewa ko farfasa akwatunan zabe da kuma hana zaben baki daya.

Wadansu kuma sun kasance sai yawo gidajen masu mulki da kuma iya rubuce-rubuce a kafafen sadarwa na zamani domin tallata gwanayensu wanda hakan ta sanya ‘yan siyasa manya da kananansu suka mayar da matasa gefe.

Masu cewa, yanzu lokaci ne na a bai wa matasa mulkin kasarnan suna da hujjojin su amma dai mafiya yawan al’umma ba su san cewa, matasa suna da manyan kalubalen da ke dabaibaye shigarsu fagen zabe ba, wadanda suka hada da kwadayin samun abin duniya da kuma rashin iyayen gida a siyasar kasar nan.

Idan aka yi waiwaye kan yadda wadanda za su shiga zaben 2023 ai matasan kadan ne suma kuma akwai manya a sama da suka daure masu gindi domin wata biyan bukata ta su da kuma yin amfani da su domin amfana da arzikin kasa cikin hikima.

Ina shawartar matasan kasar nan da su ci gaba da kasancewa masu kaunar zaman lafiya tareda neman arziki ta hanyoyi masu kyau. Sannan kada su bari ‘yan siyasa su rinka amfani da ku ana cin mutuncin al’umma ko kuma tayar da hargitsi a wajen zabubbuka da dai sauran abubuwa da matasa suka kware akai.

A karshe, yana da kyau matasa su tsaya su yi nazari domin zabar mutumin da zai kawo mafita garesu da kuma sanya su cikin madafun iko ta yadda za su taka tsanin hawa kan shugabanci wata rana wajen tafiyar da gwamnati a matakai dabandaban, tareda fatan samun dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano da kuma kasa baki daya.

Jabiru Hassan, ya ruboto wannan makala daga Dungurawa Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano. (medialink57@yahoo.com)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top