Zaben fitar da gwani: Bola Tinubu ya yi wa takwarori fintinkau-Ciki har da Osinbajo

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

A ranar Larabar jam’iyyar APC ta bayar da sanarwar lashe zaben fitar da gwani, inda tsohon gwamnan Ikko Bola Ahmad Tinubu ya lashe.

Ya lashe zaben da kuri’a 1,271 cikin 2322 da aka kada. Bisa alkaluma da aka sanar a bainar jama’a, ministan sufuri Rotimi Amaechi ya samu kuri’a 316, yayin da Yemi Osinbajo ya samu kuri’a 235, ma’ana na biyu da na uku bi da bi. Shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Lawan ya samu kuri’a 152 inda ya zo na hudu.

Gwamnan jihar Kogi mai ci, Malam Yahaya Bello ya sami kuri’a 47, shi kuwa tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha bai samu kuri’a ko daya ba.

Sai gwamnan jihar Cross Riber Farfesa Ben Ayade ya ta shi da kuri’a 37, a yayin da gwamnan Ebonyi, Mista Dabe Umahi ya samu kuri’u 38, shi kuwa tsohon gwamnan Zamfara Ahmad Sani Yariman Bakura ya samu kuri’u hudu kacal.

Tsohon gwamnan na jihar Ikko, ya mamaye muhawarar shafukan sada zumuntar a Nijeriya kusan mako guda tun kafin zaben. Zaben ya dauki hankali ‘yan Nijeriya sosai a ciki da wajen kasar, musamman bayan da ‘yan takara bakwai suka ce, sun janye wa Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *