Zabin Danmodi, alheri ga mutanen Jigawa –NURTW

Gwamnatin Namadi za ta bunkasa Jigawa ta kowane Fanni

Zababben gwamnanar Jigawa

Tura wannan Sakon

Tun bayan kammala zaben shekarar 2023, masoya da magoya baya da kuma masu fatan alheri ne ke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu a kan sakamakon zaben.

Haka kuma ake samun daidaiku da kungiyoyi na bayyana kalamansu dangane da yadda suke hasashen makomar jihohinsu karkashin jagorancin wadanda aka zaba.

Kungiyar direbobi ta kasa reshen jihar Jigawa NURTW ta bayyana cewa, zabin Danmodi da aka yi a matsayin gwamna musamman ga ‘yan asali da mazauna jihar Jigawa bisa la’akari da kyawawan manufofin da sabuwar jihar Jigawa ta zo da shi. Shugaban kungiyar, Alhaji Danjuma Sa’idu Babura ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a babban birnin jihar Jigawa jim kadan bayan kammala bikin rantsar da sabon gwamna.

Alhaji Danjuma Sa’idu Babura ya ce, zabin Malam Umar Namadi a matsayin sabon gwamna shi ne karo na farko a tarihin jihar Jigawa wanda gwamna mai ci ya mika wa sabon gwamna kuna cikin jam’iyya da ya sannan yana mataimaki ya zama gwamna.

Ya bayyana cewa lalle akwai zaman lafiya da fuskantar juna Wanda wannan shi ne jigon nasarar da ake kirgawa a yau wanda y akai ga cewar tarihi ya kammala.

“Ni zan gaya ma cewa lalle zabin da Allah yayi mana a Jigawa alheri ne ga dukkanin mutanen jiharmu, hakika muna yi wa Allah godiya bisa wannan abin alheri da ya bamu a Jigawa”.

Alhaji Danjuma Sa’idu Babura ya kara da cewa, aikin gona, ilimi da sauran sassan ayyukan ci gaban dan‘adam da kayan more rayuwa sun bunkasa a fadin jihar Jigawa karkashin jagorancin tsohon gwamna Muhammadu Badaru Abubakar saboda haka yana da kyau mutanen jihar su gode wa tsohon gwamna bisa namijin kokari domin farfado da darajar jihar Jigawa a idon duniya.

Ya kara da cewa, sabon gwamnan zai dora daga inda tsohuwar gwamnati ta tsaya. Kungiyar NURTW ta amfana daga gwamantin da ta gabata ta fuskar samun ingantattun hanyoyi domin bunkasa harkar sifiri da kuma samun sababbin motocin haya daga gwamnati domin tabbatar da ingantuwar ci gaban samun dauwamamman dorewa arziki ga mambobin kungiyar da sauran alumma.

Sai ya bukaci sabon gwamna da ya kalli hanyoyin bunkasa rayuwar al’umma domin dogaro da kai da kuma samun zaman lafiya. A karshe, ya taya tsohon gwamna Muhammadu Badaru Abubakar bisa sauke nauyin da Allah ya dora masa tare da taya sabon gwamna murnar damar karbar rantsuwar kama aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *