Zakara ya bai wa shugaban Sri Lanka sa’a

shugaban Sri Lanka
Shugaba Gotabaya Rajapaksa na Sri Lanka ya tsere daga kasar a jirgi sama na yaki, a yayin da ake ci gaba da zanga-zanga kan matsin tattalin arzikin da kasar ke fama da shi.
Rundunar sojojin sama ta kasar ta tabbatar da cewa, shugaban mai shekara 73, ya tsere zuwa Maldibes tare da matarsa da jami’an tsaro biyu. Sun isa babban birnin kasar, Male, da misalin karfe uku na tsakar dare a agogon kasar.
Tserewar da Mista Rajapaksa ya yi daga kasar ta kawo karshen mulkin da iyalansa suka kwashe fiye da shekaru ashirin suna yi a kasar.
Shugaban kasar ya buya bayan da dandazon jama’ar da ke zanga-zanga suka mamaye gidansa ranar Asabar ta makon jiya, kuma ya yi alkawarin sauka daga mulki ranar Laraba, 13 ga Yuli. Wata majiya ta ce, Mista Rajapaksa ba zai ci gaba da zama a Maldibes ba domin haka yana da niyyar zuwa wata kasar.
Dan uwansa, wanda shi ne tsohon Ministan kudin kasar, Mista Basil Rajapaksa, shi ma ya tsere daga Sri Lanka kuma an ce ya nufi Amirka.
Firayi ministan Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe, ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar sannan aka sanya dokar hana fita a lardin da ke yammacin kasar, kamar yadda mai magana da yawunsa ya fada.