Zaman Lafiya, ci gaban al’umma –Aremu

Daga Rabiu Sunusi
A ranar Talata ne kungiyar wanzar da zaman lafiya da kawo sasanci da sulhu tsakanin mutane ta jihar Kano da hadin gwiwa da kungiyar gamayyar Turai bisa jagorancin majalisar kasar Birtaniya sun gudanar da taron bita ga membobinsu bisa yadda za su shiga lungu da sako don wayar wa da al’umma kai game da amfanin zaman lafiya da sulhu a tsakanin juna.
Kungiyar da Mista Adeniyi Aremu ke jagoranta a Kano ta gudanar da taron na rana daya ne a dakin taro na Tahir Guests Palace inda ta gayyato jama’a daban daban tun daga kan jagoranci malaman addinai na Islama da bangaren Kiristoci tare da shugabanin kungiyoyin kare hakkin dan adam da jami’an gwamnati hadi da jami’an tsaro dasauran masu ruwa-da-tsaki.
Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban tafiyar Mista Adeniyi Aremu ya ce, lallai wannan hanyar ce ta dace su bi wajen wayar wa da masu ruwa-da-tsaki kai don su ma su je su tara jama’arsu domin isar da sakon.
Mista Adeniyi Aremu ya kuma kara da cewa, aikinsu ne a yanzu su sa ido tare da hada hannu da jami’an tsaro wajen yakar bangar siyasa da magance shaye-shaye da daidaito da kuma sulhunta al’umma wanda yana daya daga cikin abin da ya sa suka nemi kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya basu layukan wayar manyan jami’an ‘yan sanda (DPO) da ke kula da ofisoshin shiyya na kananan hukumomin da ke Kano domin aiki tare wajen kawar da muyagun dabi’u da magance matsalolin yau da kullum.
Shi ma Farfesa Muhammad Bello Shitu na jami’ar Bayero da ke Kano, wanda ya gabatar da mukala ya ce, sun gayyaci al’umma ne domin su bayyana hanyoyin da za su iya kawo dauki da kuma abubuwan da suke rura wutar rashin zaman lafiya.
Farfesa Shitu ya kara da cewa, wasu da yawan mahalarta taron sun bayyana cewa, yawancin rashin fahimtar da matsalar na fitowa ne daga shugabanin Addinai wajen rashin sanin yadda za su wa’azantar da mabiyansu.
Ya kuma kara da cewa, sun ja hankalin mahalarta taron yadda za su yi wajen nuna wa magoya bayansu mahimmancin zaman lafiya da yadda za su kauce wa kalaman batanci da zai iya tunzura wasu har ya kai ga tashin hankali.
A nasa jawabin, limamin masallacin juma’a na Hotoro Malam Hadi Ibrahim ya nuna matukar jin dadinsa ga wannan taron, inda ya ce, lallai Kano tana kan gaba wajen wanzar da zaman lafiya, shi ya sa mafi yawan tarurruka ake kawo su jihar. Ya kuma yi alkawarin fadakar da jama’a a lokacin sallar Juma’a kan taron domin nuna mahimmancin zaman lafiya tare da kira ga shugabani da su nuna zaman lafiya a tsakanin al’umma.
A bayaninta shugabar mata ‘yan jarida ta jahar Kano, Bilkisu Zango ta ce, lallai an gudanar da wannan taron ne a kan gabar da ake bukatarsa. Sannan ta bukaci al’umma da su kara kokari wajen wayar da kan jama’a da shugabani amfanin zaman lafiya tsakanin al’umma musamman a wannan lokaci na siyasa. Sannan ta ce, matasa da jami’an tsaro da malamai su ne kan gaba wajen wayar wa da jama’a kai kan rashin amfanin tashin hankali a cikin al’umma inda ta yi kira da cewa, kowa ya yi matukar zabura wajen koyarwa da wanzar da zaman lafiya.