Zaman lafiya ya sa na fito takarar shugabancin Dawanau -In ji Na-mai-tuwo

Zaman ya sa na fito takarar shugabancin Dawanau -In ji Na-mai-tuwo lafiya

Gwamna Abdullahi Ganduje

Tura wannan Sakon

Daga Alhussain Kano

Zaman lafiya na Daya daga cikin abin da ya sa na fito neman shugabancin Kungiyar sayar da kayan abinci na Afirka da ke unguwar Dawanau a jihar Kano, domin idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali ba za’a samu ci gaba ba, amma idan akwai zaman lafiya, komai zai gudana yadda ake so.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Daya daga cikin masu neman shugabancin Kungiyar, Alhaji Ado Na Maituwo, a lokacin da yake zantawa da manema labarai. Wani abu muhimmi da zai mayar da hankalinsa a kai matuKar Allah ya ba shi nasarar zaman shugaban Kungiyar zai yi bakin KoKarinsa wajen kwatanta gaskiya da adalci wajen tafiyar da shugabanci wanda idan Allah ya yarda ‘yan-kasuwar za su yi farin ciki da shi Alhaji Aminu Ado Na maituwo ya nuna farin cikinsa kan yadda yan-kasuwar Dawanau ke nuna Kauna da nuna zumunci musamman zaman lafiya.

Namaituwo ya ce, zai bi hanyoyin da suka kamata wajen nemo tallafi ga matsakaita da Kananan ‘yan-kasuwa daga gwamnatin jihar Kano da kuma Bankin CBN idan Allah ya yarda. Ya yi amfani da wannan dama da nuna farin cikinsa a kan yadda aka samu sabon ofishin ‘yan-sanda a kasuwar Dawanau, saboda haka zai haDa kai da su wajen inganta tsaro ta yadda ‘yan-kasuwar da baki masu shigowa za su gudanar da harkokinsu na kasuwanci cikin kwanciyar hankali da lumana .

Ya ce, haKiKa ‘yan-kasuwar na nuna masa Kauna da goyon baya musamman tun da suka ji ya fito neman matsayin a kasuwar idan Allah ya yarda ba zai ba su kunya ba a bin da yake buKata daga wurin su ita ce, addu’a tare da goyon baya, ya ce, akwai alamun samun nasara, sannan a wani zama da suka yi da waDanda za su gudanar da zaBen sun tabbatar masu da cewa, za su yi gaskiya da adalci wanda al’ummar kasuwar za su amince da shi. Zaben an tabbatar wa da Albishir cewa, an Dage zaBen zuwa 15 ga wata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *