Zaman lumana: Kano ta yi wa takwarori fintinkau- Ganduje

Tura wannan Sakon

 Daga Mahmud Sani Gambo

Gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ce, jiharsa ta kasance jihar da tafi kowace jiha zaman lafiya a Nijer­iya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake bude babban taron kungiyar editocin Nijeriya wanda take yi duk bayan shekaru biyu-biyu, wanda aka gudanar a Kano.

Ganduje ya ce, yana farin cikin karbar bakuncin taron editocin a jihar, inda ya yaba wa ‘ya’yan kungiyar sa­boda kokarin da saboda kwazonsu da aiki tukuru, inda ya shawarce su da su yi amfani da matsayinsu wajen taimak­awa kan hada kan kasar.

Yan Jaridar Nijeriya suna daya daga cikin ‘yan jaridar da suke da ‘yanci a duniya. Abin da ke da muhimmanci shi ne, su guji rashin bin ka’idar sana’ar ta su a ayyukansu, ”in ji shi.

Ya kuma tunatar da Edito­cin da cewa, su kasance masu

lura da abubuwan da ke faru­wa a kasar na rashin jin dadi, inda ya ce, lokaci ya yi, fiye da kowane lokaci, da ‘yan ja­rida za su taimaka wajen in­ganta zaman lafiya da jituwa a tsakanin mutanen Nijeriya.

Gwamnan ya kuma yi kira ga ‘ya’yan kungiyar da su ka­sance masu suka mai ma’ana alokacin gudanar da ayyukansu.

Daga karshe, ya gargadi ‘ya’yan kungiyar da su zama masu lura da hakko­kin al’umma wajen tabbatar da ‘yancinsu na aikin jarida da kuma bin ka’idojin aikin domin tabbatar da masalaha ga kowa da kowa ba tare da la’akari da kowane bambamci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *