Zamfara ta amince da hukuncin kisa kan ‘yan bindiga

Tura wannan Sakon

Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Muhammad Matawalle ya sanya hannu a kan dokar hukuncin kisa ga duk dan bindigar da aka samu da laifi a jihar, yayin da aka tanadi hukuncin daurin shekaru 20 a kan masu taimaka masu da bayanai.

Gwamnan ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar wadda ake sa rai ta taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka mamaye jihar, kuma suke ci gaba da daukar rayuka ba tare da kakkautawa ba.

Sabuwar dokar na zuwa ne kwana biyu bayan gwamnatin Zamfara ta umurci jama’a da su mallaki bindigogi domin kare kansu daga ‘yan bindigar.

Sanarwar gwamnatin ta ce, za ta taimaka wa jama’a daga masarautun jihar daban daban wajen ganin sun samu izini daga kwamishinan ‘yan sanda domin samar masu da bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *