Zamfara ta biya ‘yan-fansho fiye da biliyan 2

Matawalle ya zama jagoran APC a Zamfara

Bello Matawalle jagoran APC a Zamfara

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Gwamnatin jihar Zamfara ta biya ma’aikata da suka yi ritaya kudin fansho da albashi na Naira biliyan biyu da miliyan dari uku a Disamba, 2021.

Hakan yana kunshe ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar zamfara, Alhaji Ibrahim Magaji Dasara, ya ce, cikin adadin an biya Naira miliyan 400 ga ‘yan fansho a matsayin fansho da garatuti. Yayin da aka biya Naira biliyan 1.9 ga ma’aikata a matsayin albashinsu na Disamba 2021.

A cewar gwamnatin a watan Disambar shekarar 2021, ta biya Naira biliyan biyu da miliyan dari uku domin daidaita koma bayan da aka samu ga ‘yan fansho na rage masu wahalhalu, da kuma albashin ma’aikata.

“Gwamnati ta biya ‘yan fansho da ma’aikata, zunzurutun kudi Naira biliyan biyu da miliyan dari uku a matsayin albashin watan Disamba da fansho da gratuti a fadin jihar. Bello matawalle ya ce, “Duk da karancin albarkatun da muke da su, gwamnati za ta ci gaba da biyan ‘yan fansho kudaden garatuti, har sai an biya kowa hakkinsa.

Ya kara da cewa,”Daga yanzu kuma dole ne a biya fansho kafin biyan albashin ma’aikata duk wata.” Gwamna ya umarci ma’aikatar kudi.

Ya ce, haka kuma gwamnati ta kafa wani kwamiti mai karfi wanda ya kunZamfara ta biya ‘yan-fansho fiye da biliyan 2 shi fitattun mutane masu hankali da sanin ya kamata domin biyan duk daliban jihar Zamfara da ke karatu a kasashen ketare kudaden alawus-alawus dinsu domin samun damar ci gaba da karatunsu da kwazo. Ya kuma umarci kwamitin da ya fara biyan alawus-alawus bayan hutun sabuwar shekara.

Ya ci gaba da cewa, domin haka gwamnati na neman goyon baya da hadin kai da kuma addu’o’in jama’a domin samun dawwamammen zaman lafiya a jihar, kasan cewar matsala ce da ta fi kawo cikas ga jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *