Zamfara ta sanya wa jami’anta takunkumin magana da ‘yan-jarida

Zamfara ta sanya wa jami’anta takunkumin magana da ‘yan-jarida

Gwamna Bello Matawalle

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Gwamnatin Zamfara ta hana jami’anta da  ma’aikatu da wadansu sassa da hukumomi yin magana da manema labarai kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

Kwamishinan yada labarai na Zamfara, Ibrahim Dosara, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a  ofishinsa.

 Dosara ya ce, gwamnatin Zamfara za ta” samar da masu kula da bayanai” domin dakile yada labaran karya da ka iya ta’azzara rashin tsaro a jihar.

 Ya kara da cewa “Wannan ya kasance bisa la’akari da yanayin tsaro a jihar da kuma rashin sarrafa bayanai inda kowa ya dauki nasa ra’ayi da kuma yin nasa ra’ayi a madadin gwamnati,” in ji shi.

 Hakazalika “Majalisar ta dauki matakin ne domin ta samu iko da kuma kawar da jerin munanan bayanan da ke haifar da kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a jihar.

Kwamishinan ya ce “Daga yanzu ma’aikatar yada labarai ko kwamishinan yada labarai ne kadai yake da damar yin magana a madadin gwamnati, yayin da mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai shi ne kadai aka yarda ya yi magana a madadin gwamnan.

Ya ce  “Wadannan mutane biyu masu kula da bayanan gwamnatin jihar Zamfara ne dangane da halin da ake ciki. Ya ce “Muna kuma kira ga ‘yan jarida da su dauke shi a matsayin kayan aiki da ke kawo maku sauki wajen samun bayanan da kuke nema domin rubuta rahotanninku.

Daga karshe, ya Kara da cewa” Duk wanda ya yi magana da ku a madadin gwamnati, idan ba kwamishinan yada labarai ba ko mai bai wa gwamna shawara na musamman kan kafafen yada labarai, wannan bayanin ba shi da amfani idan ya shafi gwamnatin jihar Zamfara.” ya ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *