Zamfarawa sun tayar da kayar baya -Bayan kashe mutum, duk da biyan diyya

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
A ranar Lahadin da ta gabata aka wayi gari da wata gagarumar zanga -zanga a lokacin da al’ummar garin Nahuce a karamar hukumar Bungudu da ke jihar Zamfara, suka gudanar domin nuna rashin amincewarsu da hareharen da ‘yan bindiga suke yawan kai masu, inda suka ce, sun yi asarar mutane da dama, na baya-bayan nan shi ne wani fitaccen dan-kasuwa,
Alhaji Hadi Babangeme, duk da biyan Naira miliyan 35 a matsayin kudin fansa, sai da aka kashe shi. Al’ummar sun koka kan yadda suka biya Naira miliyan 200 kudin fansa a lokuta daban-daban ga ‘yan bindigar, inda suka jaddada cewa, har yanzu babu zaman lafiya a yankin. Zanga -zangar lumanar ta gu dana a kofar fadar gwamnatin jihar Zamfara da ke Gusau.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala zanga-zangar, jagoran masu zangazangar, Alhaji Musa Manaja ya koka da yadda mazauna garin ba sa barci da ido biyu. A cewar Manajan an yi garkuwa da wadansu mutane a ranar Asabar, yayin da wadansu kuma suka dade a hannun masu garkuwa da mutanen.
Ya ce “Kwanan nan ne masu garkuwa da mutane suka kashe wani fitaccen dan-kasuwa, Alhaji Hadi Babangeme, wanda aka yi garkuwa da shi.
Ya ce“Mutanenmu sun yi matukar kaduwa da takaici lokacin da muka ji labarin cewa, wani dan kasuwa, Alhaji Hadi Babangeme Nahuce ya mutu a hannun wadanda suka yi garkuwa da shi bayan sun karbi kudin fansa Naira miliyan 35 daga iyalansa”. Ya kuma koka da yadda jama’ar yankin Nahuce ba su da tsaro, ya kara da cewa, da dama sun gudu daga garin, “mun biya kudin fansa Naira miliyan 200 ga ‘yan fashi da makami, amma ba mu tsira ba, suna ci gaba da kai harehare tare da sace mutanen mu.” In ji Manaja.
Ya bayyana cewa, a bayabayan nan ‘yan fashin sun sace mutane 9 kuma mun biya kudin fansa, amma sun ki sakin su har sai da muka kawo masu babura kafin su samu ‘yanci. Domin haka, mutanen sun yi kira ga gwamnatin jiha, gwamnatin tarayya da jami’an tsaro da su kawo masu dauki domin kare kansu daga hare-haren da ba a saba gani ba.