Zan jajircewa wajen bai wa Gwarzo tsaro -Injiniya Abdullahi Kutama

Shugaban karamar hukumar Gwarzo, Injiniya Bashir Abdullahi Kutama
Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba
Shugaban karamar hukumar Gwarzo, Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya yi alwashin ci gaba da daukar kwararan matakan tsaro a dukkan fadin karamar hukumar. Karamar hukumar Gwarzo ta kasance wacce ta yi iyaka da jihar Katsina ta Yammacin Kano, kana mai babbar hanya wacce ta hada jihohin Katsina da Zamfara, kuma babbar cibiyar kasuwanci da ke yammacin jihar Kano.
Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya bayyana haka ga mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na ‘yan asalin karamar hukumar Gwarzo mazauna kudu maso gabas da kudu maso kudu cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Injiniya Abdullahi Kutama wanda yake wa’adi na biyu na shugabancin karamar hukumar ya ce, kasancewar karamar hukumar Gwarzo ta yi iyaka da jahar Katsina mai makwabtaka da Kano ya zame masa wajibi ya dauki matakan kare rayukan al’ummar karamar hukumar da dukiyoyinsu shi ya sa, a cewarsa, “Na jajirce wajen daukar matakan tsaro na ganin iftila’in da ya shafi makwabtan jihohin Katsina da Zamfara masu makwabtaka da jihar Kano bai fada wa karamar hukumar Gwarzo ba.
Ya kara da cewa, “AkZan jajircewa wajen bai wa Gwarzo tsaro -Injiniya Abdullahi Kutama wai bukatar ni da kai da sauran al’umma mu tashi tsaye mu bayar da gudunmuwarmu domin harkar tsaro ta tashi daga hannun jami’an tsaro ta koma tamu ni da kai da sauran al’ummar karamar hukumar Gwarzo”.
Injiniya Bashir Abdullahi Kutama, wanda shi ne sakataren kungiyar shugabannin kananan hukumonin jahar Kano (ALGON) ya ci gaba da cewa, ya tanadar da duk wasu hanyoyi na samun bayanai sosai da jami’an tsaro za a ba su na daukar matakan tsaro yadda wadancan ‘yan ta’adda ba su shigo karamar hukumar Gwarzo ba, bare ma su yi tasiri. “Alhamdu Lillah! mutanen karamar hukumata sun fahimci mahimmancin tsaro sun tashi tsaye suna bayar da gudunmuwa sannan ina yi masu godiya bisa dagewa da yin addu’a da suke yi a kan tsaro, ina rokon su da su ci gaba da yi a kara tashi tsaye, addu’a ita ce makami” in ji shi.
Da ya juya kan ayyukan da zai sanya a gaba musamman a wannan sabuwar shekarar da muka shigo, Injiniya Abdullahi Kutama ya fadi wasu daga ciki, a cewarsa, “Akwai aikin bayar da ruwan sha da ke garin Getso, abin da ya rage injin janareto da zai samar da wutar da za ta raba ruwan sha ya rage a sanya aiki ne da ya lakume sama da Naira miliyon 360”.
Ya kara da cewa, “yanzu haka akwai gina asibitoci guda uku idan ka tafi garin Nasarawa da ke Kutama. A Harin-kaura, akwai aikin asibiti, aikinsa ya yi nisa. Idan ka tafi garin Makers, aikin gina asibiti ya yi nisa. Haka ma idan ka tafi Login Kura, Shi ma aiki ya yi nisa” Ya kara da cewa, akwai wasu asibitocin da suma aikin gyare-gyaren su yana kan gaba, inda y ace, za su ci gaba da gina wasu sababbin asibitocin a dukkanin kasar dagaci, tare da samar da jami’an kiwon lafiya da za su rika kula da bayar da magunguna a wadannan asibitocin.
Daga karshe ya gode wa gwamnan jihar Kano da sarkin Karaye da hakimin Gwarzo da jami’an tsaro da dukkanin masu unguwanni da Dagatai na karamar hukumar.