Zan kawar da rashin tsaro kafin na sauka –Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, yana son ganin ya kawar da duk wata matsalar tsaro da ke addabar kasar kafin ya sauka daga mulki.
Shugaban ya fadi haka ne a wurin bikin bayar da lambobin girmamawa ga mashahuran mutanen da gwamnati ta karrama, wanda ya gudana a Abuja.
Ya ce, yana son ya jaddada alwashin da ya sha a lokacin bikin tunawa da ranar samun ‘yancin kai na kasar, cewar burinsa shi ne ya mika wa shugabannin da za a zaba, kasar, ba tare da wata matsalar tsaro ba.
A lokacin bikin karramawar shugaba Buhari ya kuma tunatar da wadanda suka samu lambar girmamawar cewa, ba an ba su ita ne domin kwalliya ba, sai domin tunatar da su nauyin da ke kansu a matsayin ‘yan kasa nagari.