Zargin satar babur: Fusatattun matasa sun kone wanda ake zargi har lahira a Warawa

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Wani barawon babur ya kone kurmus a Garin Da’u na karamar hukumar Warawa, jihar Kano.

Majiyar Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa kwamandan kungiyar ‘yan banga na tsaro Muhammad Kabir Alhaji ya fada wa manema labarai a ranar Talata cewa an kashe wanda ake zargin ne a ranar Litinin bayan da gungun mutanen suka gan shi ya saci babur a bankin Zenith na reshen Wudil.

Ya ce yayin da wanda ake zargin ya yi kokarin tserewa da babur din, sai mutane suka fara ihu, da gudu suka riske shi a garin Da’u.

Kabir Alhaji ya ce kafin jami’an tsaro su iso wurin, mutanan sun yi amfani da tayoyi da fetur suka kuma kona shi da ransa.

A cewarsa, duk kokarin kubutar da wanda ake zargin ya ci tura domin ya mutu kafin isowar jami’an tsaro.

Ya ce ‘yan bangar sun tattara gawar wanda ake zargin tare da mika shi ga ofishin rundunar yan sanda na karamar hukumar Warawa.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa manema labarai cewa ba a ba shi labarin abin da ya faru ba kuma ya yi alkawarin dawowa idan ya samu cikakken bayani daga bangaren Warawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *