Zidane na gab da maye gurbin Pochettino

Zinedine Zidane
Kungiyar PSG na kasar Faransa na gab da cimma yarjejeniya da Zinedine Zidane a matsayin sabon cocinta da zai maye gurbin Mauricio Pochettino.
A cewar gidan radiyon Europe 1, kungiyar na kan tattaunawa domin tsohon kocin na Real Madrid mai shekaru 49 ya koma PSG kafin sabuwar kakar wasanni.
Da Kamfanin dillancin labaran AFP ya tuntubi majiyar PSG, ta ki amincewa ko ta musanta rahotannin.
Kwantiragin Pochettino bai kare ba.
Pochettino dai yana da sauran shekara guda kan kwantiraginsa da PSG kuma ya jagoranci kungiyar da Katar ke marawa baya samun nasara a gasar Ligue 1 a kakar da aka Karkare, to amma Real Madrid ta fitar da su daga gasar zakarun Turai a zagaye na ‘yan 16.
Burin lashe Gasar Zakarun Turai
Masu kulob din na Katar na da burin lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta Turai kuma Zidane ya jagoranci kungiyar ta Spain ta lashe kofin kaka uku a jere tsakanin 2016 da 2018.
Tsohon dan wasan da ya lashe gasar cin kofin duniya da Faransa a shekarar 1998, Zidane ya lashe gasar zakarun Turai a lokacin da yake dan wasa a Real a 2002.