Ziyarar San-kano a Kalaba

San-Kano Aminu Ado

Tura wannan Sakon

Daga Musa muhammad Kutama, Kalaba

Yadda ’yan Arewa mazauna garin Kalaba suka fantsama ganin Sarki hakika ko tababa babu al’ummar asalin Arewacin Nijeriya mazauna jihar Kuros-riba sun nuna matukar farin ciki da yin tozali da Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a birnin na Kalaba.

Sai dai ziyarar ba ta buga haraji ko jangali ba ce ga talakawa da sarakuna a lokutan baya suke yi domin umartar hakimai da dagatai su karbi haraji ba, a’a, jami’ar Kalaba ce ta gayyato shi a matsayinsa na shugaban jami’ar, a bikin yaye dalibai karo na 35 da aka yi a makon jiya a harabar makarantar.

’Yan Arewa mazauna garuruwan kudancin kasar nan da kuma jama’ar kudanci ne suka rika yin tururuwa zuwa garin Kalaba da kuma jami’ar domin su ga sarkin mai matukar farin jini da kwarjini a idon al’umma.

Shi kuwa wakilinmu, tsundum yana cikin tawagar abokan aiki ‘yan uwansa ’yan jarida, kana mataimakiyar shugabar jami’ar, Farfesa Florence Obi ta gaya wa manema labarai ana gab da fara bikin yaye daliban, ganawar da ta yi da su cewa, makarantar za ta gwangwaje Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da digirin digirgir tare da wasu fitattun ‘yan Nijeriya da suka hidimta wa kasa.

A jawabinsa, shugaban jami’ar, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tabo nasabarsa da tushensa cewa, shi jika ne ga shahararriyar masarautar nan ta Ilori da ke jihar Kwara. Tun da farko, a ziyarar da Alhaji Aminu Bayero ya kai wa takwaransa, babban basaraken Kuros-riba, Obong Edidem Ekpo Abasi Otu, Bayero ya jaddada mahimmancin da zaman lafiya yake da shi, inda ya nuna wa basaraken na Kalaba murna bisa irin yadda ‘yan Arewa mazauna jihar Kuros- riba suke zaune lafiya.

A harabar dakin taron, an ga irin yadda ‘yan asalin jihar Kuros-riba suka rika daukar hotuna tare da sarkin Kano, abin ya matukar kayatar da su da ba su sha’awa.

A washe gari, Juma’a, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ziyarci unguwar Hausawa da ke birnin Kalaba, inda ya yi sallar Juma’a a masallacin Juma’a na unguwar Alhaji Hamisu Dan Mudi mai adashi. Sarkin Sharifan Kalaba da Alhaji Hashimu Ibrahim Mai Agogo, shugaban al’ummar Arewa maso yamma a garin Kalaba na daga cikin wadanda suka yi wa Mai martaba sarkin Kano hidima.

Haka kuma, sarkin Hausa-Fulani da ke Nasarawa-Bakoko, karamar hukumar birnin Kalaba, nadaya daga cikin wadanda suka rufa wa sarkin Kano baya wajen sallatar Juma’ar a wannan rana. Daga cikin ayarin sarkin Kano akwai gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, Shi ma ya yi tsokaci game da zamantakewa da kuma wasu al’amuran da suka jibinci jihar da ma bayanin masarautun da ya kirkiro na sarakunan yanka, inda ya kara da cewa, masarautun mahadi ne kadai ka iya ture su.

Jim kadan bayan raka Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa filin jirgin saman kasa da kasa da ke Kalaba a yammacin Asabar, Alhaji Hashimu Ibrahim, shugaban al’ummar jahohin Arewa maso yammacin Najeriya ya gana da manema labarai inda ya nuna matukar farin ciki da zuwan sarkin inda ya ce, “Mun yi matukar farin ciki da wannan ziyarar da Mai martaba sarkin Kano ya kawo mana, har ya yi sallar Juma’a da mu a unguwar Hausawa”.

Ya ci gaba da cewa, “Mun yi godiya da addu’a da nasihar zaman lafiya da ya yi mana, muna rokon Allah ya saka masa da alheri ya mayar da shi gida shi da tawagarsa lafiya”. Alhaji Ibrahim Mai Agogo, shugaban kungiyar ‘yan asalin jahohin Arewa maso yammacin Nijeriya ya ce, hakika ziyarar ta kara nuna darajar mutanen Arewa mazauna jihar Kuros-riba a idon al’ummar jihar.

Shi Kuma Alhaji Hamisu ‘Dan Mudi Mai Adashi (Sarkin Sharifan Kalaba) wanda shi ne shugaban kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam a yankin kudu maso kudu ya ce, hakika ziyarar sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ta kara nuna darajar ‘yan Arewa mazauna Kuros-riba, musamman irin yadda ake zaune da juna girma da arziki, sannan da daukacin al’ummar da yake shugabanta.

Ya ce, “Sarki na kowa ne, mun ji dadi sosai da har ya zo nan aka yi sallar Juma’a da shi da kuma takaitacciyar nasiha da ya yi mana kan zaman lafiya da mutunta juna” a cewar Sarkin Sharifan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *