Zulum ya koka da karancin albashin malaman firamare -Saboda karbar kasa da Naira dubu 11

Gwamnna Babagana Zulum
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya koka kan rashin aiwatar da mafi karancin albashi a bangaren malaman makaranta ga ma’aikatan kananan hukumomi (LEA) a jihar, inda ya nanata cewa, har yanzu wasu suna karbar kasa da Naira dubu 11 a matsayin albashin wata-wata.
Wannan ya biyo bayan sukar da ake yi wa gwamnatin jihar kan gazawarta na cika alkawuran da ta dauka na aiwatar da sabon mafi karancin albashi a matakin kananan hukumomi ga ma’aikatan da kuma hukumar ilimi ta kananan hukumomi (LEA) da kundin tsarin mulki ya tanada na biyan albashin malaman firamare.
Idan za a iya tunawa cewa, cibiyar bincike ta Duniya (ICIR) a ranar Talata, 26 ga Oktoba, 2021, ta buga wani labari da ke tabbatar da cewa, sama da watanni 10 ko shekara guda da suka wuce, ana ci gaba da biyan malaman LEA a jihar Borno a bisa mafi karancin albashi a matakin kananan hukumomi.
Kodayake rahoton ya yi nuni da cewa, gwamna Zulum ne ya fara kuka a bainar jama’a cewa, har yanzu malamai a matakin kananan hukumomi (LEA) na samun kasa da Naira dubu 11, yayin da sauran takwarorinsu da ke aiki a matakin jiha ake biyansu kan Naira dubu 30 a matsayin tsarin sabon mafi karancin albashi.
Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, a ranar Litinin ne ya bayyana hakan a yayin da yake mayar da martani ga wasu hotuna da aka yi ta yadawa a shafukan sa da zumunta, inda suka nuna albashin wasu malaman LEA, wadanda ke da kasa da Naira dubu 10 a matsayin albashinsu na wata-wata.
Kakakin na gwamna ya kara da cewa, gwamna Zulum ya yi jawabi ne a lokacin da yake jawabi ga sabuwar hukumar ilimi ta bai-daya ta jihar Borno, karkashin sabon shugabanta, Farfesa Bulama Kagu, a gidan gwamnati da ke Maiduguri, a ranar 26 ga Oktoba, 2021.
A lokacin gwamnan ya ce, “Abin takaici ne a ce akwai malaman da har yanzu suke karbar tsakanin Naira dubu 11 zuwa Naira dubu 13 da ma kasa da haka. Duk da kalubalen da ake fuskanta na tattalin arziki, dole ne mu himmatu wajen ganin cewa kowane malamin da ya cancanta a jihar Borno ya sami mafi karancin albashin Naira dubu 30, wanda shi ne mafi karancin albashi na kasa.” Zulum ya ambata.
Gusau ya tunatar da cewa, Zulum da kansa ya amince cewa, duk da cewa an riga an fara aiwatar da mafi karancin albashi ga dukkan ma’aikata a matakin gwamnatin jihar ciki har da malamai, aiwatar da shi a LEA za a iya yi ne kawai bayan an tsaftace tsarin kamar yadda ake yi wa ma’aikatan jihar, inji Gusau.
Ya ce, “Domin shirya malaman LEA don biyan mafi karancin albashi na kasa, gwamna Zulum ya kafa kwamitin da zai gudanar da jarrabawar karatu da kuma tantance cancanta a kan dukkanin malaman na LEA su sama da dubu 17 a fadin kananan hukumomin jihar 27.
“A ranar 17 ga Fabrairu, 2022, kwamishinan ilimi na Jihar, Injiniya Lawan Abba Wakilbe, kwararre ne, kuma masanin ilmi, wanda ya jagoranci kwamitin, ya gabatar da abin da Zulum ya bayyana a matsayin rahoto mai ban tsoro”.
“Kwamitin ya gano cewa, daga cikin malamai dubu 17,229 da ake da su, malamai dubu 11,790 ne aka samu ba su cancanci su koyar ba, wanda yake wakiltar kashi 69 cikin 100 na daukacin malaman na LEA”.
“Tare da wannan rahoto, akwai wani kwamiti mai karfi na musamman da gwamna ya kafa karkashin jagorancin wani jami’i, Dokta Shettima Kullima, gwamna Zulum yana da zabin korar malaman da ba su cancanta ba su 11,790, ba kuma zai iya amfani da kudaden da ake amfani da su a matsayin albashinsu, domin aiwatar da mafi karancin albashi na kasa ga kwararrun malamai dubu 5439, amma ya ki yin hakan duk da tsammanin da jama’a ke yi na sallamar su”.
A cewar kakakin gwamnan, duk da haka, Zulum ya sanar da cewa, babu daya daga cikin malamai da ba su cancanta ba da za a sallama domin haifar da karin rashin aikin yi, a maimakon haka, ya dauki matakin jinkai don kauce wa karuwar rashin aikin yi a jihar Borno.
Ya kara da cewa, a maimakon haka, gwamnan ya gano ko ya zabo wasu da dama daga cikin malaman firamare da ba su cancanta ba domin horar da su a kan aikin yayin da wasu kuma za a tura su aiki a sassa dabandaban na ma’aikatan kananan hukumomi da na jiha da suka hada da bangaren dashen itatuwa a karkashin ma’aikatar muhalli ta jihar.
Bisa rahoton kwamitin kuma, gwamnan ya bayar da umarnin aiwatar da sabon mafi karancin albashi domin yin amfani da shi ga kwararrun malaman LEA dubu 5439 da aka gano cewa sun cancanci koyarwa.