Zulum ya rarraba kayayyakin tallafi a yankin Gwoza

Sani Gazas Chinade Daga Damaturu
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya rarraba kayayyakin tallafi ga al’ummomin da ke yankin Gwoza da suka hada da garuruwan Ngoshe, Warabe da Pulka, da ke qaramar hukumar ta Gwoza, a kudancin lihar.
Gwamna Zulum kafin haka sai da ya yada zango a garin Ngoshe, domin sanya ido kan aikin rarraba tallafin kayan abinci da kudi fiye da Naira miliyan 24 ga mabuqata 1,200, ‘yan gudun hijira wadanda suka dawo garuruwan su daga Pulka da Maiduguri.
Gwamnan ya jagoranci miqa wa kowane magidanci buhun masara mai nauyin kilo 50, buhun dawa kilo 50, da na wake mai nauyin kilo 25, shinkafa kilo 12.5, man girki lita 5, da sauran kayan alatu tare da Naira dubu 20,000.
Gwamnan ya bayyana cewa, wannan tallafi ne wanda za a ci gaba da aiwatar da shi domin qarfafa gwiwar ‘yan hijirar da suka koma yankunan su, kana kuma hakan zai taimake su wajen samun damar ci gaba da ayyukan su na noma domin dogaro da kansu.
Bugu da qari, al’ummar qauyen Ngoshe sun koma garin tun 15 ga Oktoban 2020, bayan aikin inganta yanayin tsaro a yankin.
Har ila yau gwamnan ya kai ziyarar gani da ido ga aikin samar da kayan karatu a makarantar firamaren garin Ngoshe wanda hukumar bayar da ilimin bai daya a jihar ke gudanar da shi tare da qoqarin sake bude makarantar nan da mako biyu masu zuwa, aikin ya kai matakin kaso 95 cikin dari na kammaluwar aikin.
Gwamnan ya qara duba aikin ginin cibiyar kiwon lafiya mataki na farko a garin na Ngoshe, wanda ya buqaci dan kwangilar ya tabbatar ya kammala aikin a daidai lokacin da aka qulla yarjejeniya da shi, domin bunqasa kiwon lafiyar al’ummar yankin.
Daga nan gwamnan ya zarce zuwa garin Warabe, shi ma a qaramar hukumar Gwoza inda ya kai ziyarar gani da ido a aikin gina gidaje 350 wadanda gwamnatin jihar ke ginawa, wadanda mayaqan Boko Haram suka lalata su.
Zulum sai ya dasa aya a ziyararsa a garin Pulka, wanda a can ya duba yadda aikin ginin makarantar sakandare ta zamani a garin domin zuwa daidai da zamani.