Zulum ya yi alkawarin taimaka wa jami’an tsaro -A kowane lokaci

Zulum ya yi alkawarin taimaka wa jami’an tsaro -A kowane lokaci

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum

Tura wannan Sakon

Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

A kokarin da yake yi na ganin harkokin samar da tsaro ya ci gaba da ingantuwa gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya alkawarta ci gaba da taimaka wa dukannin bangarorin jami’an tsaro da na matasa ‘yan sa kai da ke jihar don ganin an kawar da duk wani take-take na ‘yan kungiyar Boko da suka shafe fiye da shekaru 12 suna addabar jihar da ma jihohin makwabta da kuma kasashen da ke kewaye da jihar.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na sabuwar shekara ga al’ummar jihar, ya kara da cewa, “gwamnatinsa ta shirya tsaf domin ci gaba da tallafa wa rukunonin jami’an tsaron da ke jihar da kuma na ‘yan sa kai da ke cikin al’umma domin ganin sun gudanar da ayyukan da suke yi na yaki da ‘yan Boko Haram da sauran laifuffuka cikin nasara.”

Ya kara da cewa, “wani bangare na dabarun da muke dauka wadda muka yi gum da bakinmu shi ne yadda muka shirya tare da tsara rurrufe sansanonin ‘yan gudun hijira da ke babban birnin jihar Maiduguri da wadansu yankunan jihar duk da kafin hakan sai da muka sanar yin haka cikin hikima cikin kankanin lokaci.”

“Domin haka mun rufe sansanonin ‘yan gudun Hijirar ne domin bayar da dama ga al’ummomin da ke sansanonin su zama masu dogaro da kansu, domin rayuwa a wadannan wurare ba abin bukata ba ne gare mu. Domin haka dogaro da kai shi ne babban abin alfahari ga kowace irin al’umma.”

“Kuma sanin kowa ne cewar, sansanonin ‘yan gudun hijira wurare da aksari a kan samu munanan dabi’u ciki wadda kan haifar da aikata abubuwa abin ki suka hada da shaye-shaye, karuwanci, fade, da wadansu ayyukan ta’ddanci.”

“Saboda haka babu wani shugaban da ya san abin da yake yi da zai bar al’umma na ci gaba da rayuwa cikin irin wannan hali ba tare da ya dau mataki a kai ba.”

Samar da ire-iren wadannan sansanoni na ‘yan gudun hijira na samuwa ne sakamakon wata annoba ko wani rikici ko dai wani ‘ibtila’i da ya faru kan wadansu al’’ummomi kamar yadda ya faru ga al’ummar muna rikicin Boko Haram. To amma ba ana samar da shi ba ne haka siddan.

“Domin haka lokaci ne ya yi na jama’ar da ke rayuwa a sansanonin aka umarce su da barin wuraren ganin cewar, waccar matsalar ta rashin tsaro a yankunansu na gab da zama tarihi koma muce ta zama a mafi yawan yankunan. Saboda haka wannan shi ne lokacin da ya dace da daukar matakin mayar da ‘yan hijira garuruwan su na asali domin ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba tun fil azal.”

“Rufe sansanonin ‘yan gudun hijira da muka yi mun yi koyi ne da irin yadda ake gudanarwa a bangarorin duniya da dama, kuma mun yi ne bisa ga tsari, kuma za mu ci gaba da jin koke-koken jama’a musamman wadanda ke da shawarwarin ciyar da jihar gaba.”

Daga karshe, gwamna Zulum ya kara da cewa, gwamnatinsa ba ta duba ga zaben 2023 da ke tafe kasancewar ba shi ne gabansa ba, duk da cewa, wadansu na aiki ne domin zaben 2023 yayin da wadansu kuma ke yi domin Allah da zimmar sauke nauyin da ke kan su kamar yadda muma irin akidar muke nan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *