Zuwa ga ‘yan APC, Zamfara: Yari ya yi nasiha kan aiki tare

Zuwa ga ‘yan APC, Zamfara: Yari ya yi nasiha kan aiki tare
Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Ina shawartar shugabannin jam’iyyar da su tsara dabarun yadda za su wayar da kan mutane game da muhimmancin yin aiki tare kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyya ya tanada”.

Abdul’aziz Yari Abubakar ya bayyana hakan a lokacin da yake karbar bakuncin shugaban jam’iyar APC na jihar Zamfara, bangaren Bello Matawalle, Alhaji Tukur Danfulani a lokacin da suka ziyarceshi domin kai masa gaisuwar goyon baya a gidansa. Ya kara da cewa, fatan sa shi ne cewa, jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya kuma jam’iyya daya tilo da ta yi nasara a jihar Zamfara.

Ya kuma bukaci wadanda suka ji bacin rai sakamakon sulhun da su dauki hakan a matsayin wani aiki na Allah. Ya kuma yi kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar da su amince da sulhun cikin gaskiya da adalci, su kuma yi aikin su kuma ci yar da jihar gaba.

Ya kuma bayyana sulhun da aka yi a jam’iyyar a matsayin hanyar ci gaban Zamfara da jam’iyyar da kasa baki daya . Yari ya gode wa Allah bisa kokarin sulhu da aka yi, inda ya bukaci mabiya da su ci gaba da gudanar da wannan nasara ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai ga ci gaban jam’iyyar.

Da yake jawabi a yayin ziyarar, Danfulani ya shaida wa Yari cewa, shugabancin jam’iyyar a jihar ya yi matukar farin ciki da samun karbuwar da ya yi masa ta irin gagarumin tarbar.

Danfulani ya kara da cewa, a matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar a kasar nan, APC ba za ta iya rabuwa da tsohon gwamnan ba, wanda karimcinsa da kyakkyawan shugabanci da kuma kwarewarsa ta siyasa ce da ba za a iya wasa da ita a Zamfara ba.

Ya kuma bukaci jiga-jigan jam’iyyar APC da su tabbatar da cewa, hadin kan da aka samu ya dore da kuma kare mutuncin ‘ya’yan jam’iyyar da suka shigo jam’iyyar musamman a yanzu da kasar nan take tunkarar zabe.

Shugaban ya ce, “Ina ba da tabbacin cewa, zan ci gaba da bin gaskiya da adalci a cikin shugabancina yadda ake yi wa dukkan mambobin jam’iyar adalci” ya ce”Jam’iyyar kuma za ta tabbatar da da’a da mutunta shugabanni a kowane mataki”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *